Obasanjo Ya Yi Sabuwar Fallasa Kan Majalisar Dattawa da Ta Wakilai

Obasanjo Ya Yi Sabuwar Fallasa Kan Majalisar Dattawa da Ta Wakilai

  • Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya zargi ƴan majalisar dokokin tarayya da ƙayyade albashin da za a biya su da kansu
  • Obasanjo ya kuma yi zargin cewa ɓangaren zartaswa na ba ƴan majalisar tarayya abin da bai cancanta ba kuma suna sanya hannu su karɓa
  • A cewar tsohon shugaban, ƴan majalisar sun karɓi Naira miliyan 200 kowannen su, inda ya ƙara da cewa hakan ba daidai ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya zargi ƴan majalisar dattawa da ta wakilai da ƙayyade albashinsu da kansu.

Obasanjo ya bayyana cewa hakan ba daidai ba ne kuma ya saɓawa kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bayyana dalilin kasa cafke 'yan bindigan da ke nuna kansu a duniya

Obasanjo ya caccaki 'yan majalisa
Obasanjo ya fadi kuskuren 'yan majalisa Hoto: @LegendaryJoe, @Oolusegun_obj
Asali: Twitter

Obasanjo ya caccaki ƴan majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon shugaban ƙasan, ƴan majalisar tarayya sun samu Naira miliyan 200 kowannensu, kuma sun sanya hannu sun karɓa, cewar rahoton Channels tv.

Obasanjo ya ƙara da cewa ba daidai ba ne ƴan majalisar su riƙa tsara albashinsu da kansu.

"A ɓangarenku, tare da mutuntawa, bai kamata ku ƙayyade albashinku ba. Amma ku ne kuke yanke abin da za a biya ku, alawus ɗin da kuke ba kanku, alawus ɗin jarida."
"Kuna ba kanku abubuwa da dama sannan kun san cewa hakan bai dace ba."
"Kuna yin hakan, majalisar dattawa na yin hakan sannan kuna yin alfahari da hakan. A wasu lokutan ɓangaren zartaswa yana ba ku abin da ba ku cancanta ba. Dukkanin ku an ba ku N200m."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya karɓi baƙuncin ƴan majalisar wakilai

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo ya fadi hanyar da Najeriya za ta samu ci gaba

Obasanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu ‘yan majalisar wakilai shida ƙarƙashin jagorancin Ugochinyere Ikenga a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta.

Ƴan majalisar dai sun je ne domin neman goyon bayan tsohon shugaban ƙasan kan ƙudirin samar da wa’adin mulki ɗaƴa na shugaban kasa da gwamnoni na shekara shida a majalisar tarayya.

Karanta wasu labaran kan Obasanjo

Obasanjo ya ba shugabanni shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan batun kawo tsarin wa'adin mulki ɗaya na shekara shida.

Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya ba za ta samu ci gaban da take buƙata ba har sai shugabanni da al'ummarta sun sauya ɗabi'unsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng