Kotun Koli Ta Sake Kassara Gwamnoni 36 Bayan Sabon Umarni kan Kananan Hukumomi

Kotun Koli Ta Sake Kassara Gwamnoni 36 Bayan Sabon Umarni kan Kananan Hukumomi

  • Kotun Koli da ke Abuja ta sake ba da umarni bayan hukuncin da ta yi kan 'yancin kananan hukumomi a Najeriya bayan korafin Gwamnatin Tarayya
  • Kotun ta umarci ba kansiloli da shugabannin kananan hukumomi a Najeriya wa'adin shekaru hudu kamar yadda gwamnonin jihohi ke yi
  • Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun ta yi kan ba kananan hukumomin 'yancinsu yayin da gwamnonin jihohi ke dakile su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta ba da sabon umarni game da hukuncin da ta yanke kan kananan hukumomi a Najeriya.

Kotun ta ba da umarnin cewa dole kowane kansila ko ciyaman ya shafe shekaru hudu a kan mulki kamar gwamnoni.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tsohon gwamnan Kano ya gano bakin zaren, ya aika saƙo ga Tinubu

Kotun Koli ta ba da sabon umarni bayan hukuncin kananan hukumomi
Kotun Koli ta umarci ba kansiloli da shugabannin kananan hukumomi wa'adin shekaru 4 a mulki. Hoto: Supreme Court.
Asali: Facebook

Sabon umarni kan wa'adin shugabannin kananan hukumomi

Tribune ta tattaro cewa wannan umarni na kunshe ne a cikin kwafin takardar CTC da Mai Shari'a Mohammed Garba ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba da sauran alkalai guda shida ne suka yanke hukuncin tun a ranar 11 ga watan Mayun 2024 da muke ciki.

Alkalan suka ce gwamnoni suna amfani da karfin ikonsu wurin gallazawa ciyamomin wanda ke hana su gudanar da mulki yadda ya dace, cewar Punch.

Kotun ta yi korafi kan halin gwamnoni

Sun bayyana halin da kananan hukumomi suke a kasar da abin takaici duba da yadda daya bangaren ke musgunawa daya.

Har ila yau, Alkalan suka ce ciyamomin da kansiloli suna da goyon baya daga kundin tsarin mulkin 1999 na Najeriya.

Suka ce duba da kundin tsarin mulki, abin takaici ne yadda gwamnoni suka yi fatali da dokar gudanar da zabe kamar yadda yake a dokokin Majalisun jihohi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara daukan matakin ragewa talaka raɗaɗin cire tallafin man fetur

Kotu ta yi hukunci kan kananan hukumomi

A baya, kun ji cewa Kotun Koli a Abuja ta yi zama kan korafin Gwamnatin Tarayya game da kananan hukumomi a Najeriya.

Kotun ta umarci Gwamnatin Tarayya ta rika ba kananan hukumomin kasonsu daga asusunta kamar yadda take yi wa gwamnoni.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta shigar da korafi kan gwamnonin Najeriya 36 da ke fadin kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.