Kano: Bidiyon Yadda Aka Yi Salloli da Addu'o'in Neman Mafita Kan Tsadar Rayuwa

Kano: Bidiyon Yadda Aka Yi Salloli da Addu'o'in Neman Mafita Kan Tsadar Rayuwa

  • Yayin da ake cikin wani irin mayuwacin hali a Najeriya, wasu mazauna jihar Kano sun gudanar da addu'o'in neman sauki
  • An gudanar da addu'o'in ne da karatuttukan Alkur'ani mai girma domin neman mafita daga wurin Ubangiji Mai girma a kasar
  • Wannan na zuwa ne yayin aka shafe kwanaki ana zanga-zanga a fadin kasar saboda halin kunci da tsadar rayuwa da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wasu mazauna jihar Kano sun gudanar da addu'o'i da salloli saboda halin kunci da ake ciki.

An gudanar da karatuttukan Alkur'ani mai girma da kuma addu'a a wurare daban-daban a fadin jihar.

An gudanar da addu'o'in neman mafita a jihar Kano
Wasu mazauna Kano sun gudanar da addu'o'i da karatuttukan Alkur'ani domin neman mafita. Hoto: @Idrisawa/@Nigerianstories.
Asali: Twitter

Kano: An gudanar da addu'o'in neman sauki

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, Abba ya dauko muhimman ayyuka 7 domin farfaɗo da Kano

Daily Trust ta tattaro cewa an gudanar da addu'o'in ne a Yankaba da Daurawa da Gyadi-Gyadi da Hausawa Sabon Titi da Panshekara da Tudun Murtala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gudanar da addu'o'in na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa a fadin kasar.

Tun bayan fara zanga-zanga wasu ke kiran a gudanar da salloli da addu'o'i domin neman mafita a wurin Ubangiji.

Duk da haka wasu na ganin hakan ba shi ne mafita ba saboda wasu ƙasashe ba hanyar da suka bi ba kenan suka samu cigaba.

Musabbabin gudanar da zanga-zanga a Najeriya

Wannan mataki ya biyo bayan fantsama kan tituna da matasa suka yi domin neman gwamnati ta dauki matakin gaggawa.

Sai dai duk da zanga-zangar da aka yi a fadin kasar, gwamnatin ba ta dauki mataki ko da guda daya daga cikin korafinsu ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Majalisar matasan Arewa ta yi fatali da neman dauke cibiyar NCC daga Kano

APC ta yi zargi kan rabon shinkafa

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da shinkafar Gwamnatin Tarayya da wasu jami’ai suka yi.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci da a gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kwamitin bincike mai zaman kansa.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, ya nuna damuwarsa kan yadda wasu jami’an gwamnati suke ci gaba da karkatar da kayan tallafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.