Matasa Sun Daka Wawa Kan Mota Dauke da Takin Zamani, Ciyaman Ya Fadi Mai Laifi

Matasa Sun Daka Wawa Kan Mota Dauke da Takin Zamani, Ciyaman Ya Fadi Mai Laifi

  • An tafka asara bayan babbar mota makare da takin zamani ta gamu da matsala a jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya
  • Matasa sun yiwa motar tas bayan ta yi gamu da hatsari a kusa da fadar Sarkin Demsa a karamar hukumar
  • Shugaban karamar hukumar, Hon. Akam Sanda Jallo ya tabbatar da lamarin a yau Asabar 10 ga watan Agustan 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Wasu matasa sun farmaki babbar mota dauke da takin zamani inda suka afka mata.

Motar na makare da takin zamani a kan hanyarta ta zuwa karamar hukumar Demsa da ke jihar Adamawa.

An wawashe mota dauke da takin zamani a Adamawa
Matasa wawashe babbar mota da ta dauko takin zamani a jihar Adamawa. Hoto: Ahmadu Fintiri.
Asali: Twitter

Adamawa: Matasa sun dakawa motar taki wawa

Kara karanta wannan

Ana tsaka da bankadar Dan Bello, Tinubu ya dakatar da aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri

Tribune ta tattaro cewa an yi wawan takin zamanin ne a kusa da fadar basaraken garin bayan motar ta yi hatsari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da motar na dauke da takin zamani buhu 600 wanda gwamnatin jihar ta samar domin bunkasa harkar noma.

Shugaban karamar hukumar, Hon. Akam Sanda Jallo ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 10 ga watan Agustan 2024.

Hon. Jallo ya ce laifin mai kawo kayan ne saboda bai tuntube shi ba kafin taho da kayan karamar hukumar, cewar Daily Post.

An gano wadanda suka kwashe takin zamani

Shugaban karamar hukumar ya ce takin na daga cikin tallafin gwamnatin jihar da aka ware musu a Demsa.

Ya ce da an fada masa kafin taho da kayan da tuni ya samar da wuri mai tsaro domin adana kayan zuwa wani lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya taso masu zanga zanga a gaba, ya yi kakkausan kashedi

Har ila yau, ya ce an gano wadanda ke zuga matasan su kwashe kayan da aka samar domin manoma.

Matasa sun tafka barna kan motar abinci

Kun ji cewa Miyagu akalla 100 ne suka farmaki motar bas dauke da kayan tallafin abincin da wata kungiya a jihar Cross River.

Bas din makare take da kayan abinci na kungiyar ƴan jaridu a jihar da ta nufi sakatariyar kungiyar domin jibge su.

Hakan na zuwa ana saura kwana ɗaya a fara zanga-zanga a fadin Nigeria a ranar 1 ga watan Agustan 2024 saboda halin kunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.