Wasu Baram Barama 8 da Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio Ya Yi gaban Duniya
Abuja - Godswill Akpabio shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya tun watan Yunin 2023, kuma tsohon ministan Neja-Delta ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bayan rike wadannan mukamai, Godswill Akpabio ya yi kwamishina har ya zama gwamna a jiharsa ta Akwa Ibom na shekaru takwas.
Mukaman da ya rike ba su hana Sanata Godswill Akpabio sakin layi ba, an saba rahoto shi yana kauce hanya a wajen magangansa.
Legit ta bibiyi lokutan da Godswill Akpabio ya jawo abin magana a dalilin kalamansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Kudin hutun ‘yan majalisa
Watanni biyu da zamansa shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya yi subutar baki a gaban duniya, ya ce an aikawa ‘yan majalisa kudin hutu.
Kafin Akpabio ya ankara, ‘yan jarida sun dauki wannan magana da ya yi. Lamarin dai ya fusata irinsu Sanata Ali Ndume tun a lokacin.
2. 'Tinubu ya rabawa jihohi kudi' - Akpabio
An rahoto Akpabio yana ikirarin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya aikawa kowace jiha N30bn domin a magance matsalar yunwa da talauci.
Daga baya dole hadiminsa ya lashe wannan amai da ya kwaba, ba a ba wadannan kudi masu yawa da tsohon gwamnan Akwa Ibom ya fada ba.
3. Akpabio: 'A bar talaka ya sarara'
Jaridar Vanguard ta taba rahoto Akpabio yana wani bayani da wasu su ka dauke shi a matsayin izgili da talakawan da su ke cikin kunci.
Shugaban majalisar ya yi ta maimaita zancen ‘a bar talaka ya sarara’, wasu su na ganin shakiyanci ne kurum ba wai tausayin talaka ba.
4. Mafi karancin albashi
Daily Trust ta kawo labarin Sanata Akpabio ya na cewa dole duk wanda aka dauke shi aiki ko da a gida ne, sai an biya shi akalla N70, 000 a wata.
Shugaban majalisar ya fadi haka ne ganin an sa hannu a sabon mafi karancin albashi. Daga baya bincike ya nuna ba haka dokar kasa ta ce ba.
5. Kalaman Akpabio gabanin zanga-zanga
Magangunan da ya yi daf da za a shiga zanga-zanga ya hurawa lamarin wuta, an ji ya na cewa a tafi zanga-zangar, su na nan su na cin abinci.
Akpabio ya sha sukar har daga kungiyar Amnesty Internal saboda wannan zance a mawuyacin hali, bai lura da kujerar da yake kai ba.
6. Murde zabe a lokacin PDP
A rahoton Premium Times, ana tunawa da lokacin da ‘dan siyasar ya fito fili yana fadawa duniya yadda su ka murde zabe a jihar Akwa Ibom.
An taba daukar shi a taron PDP yana bayanin ya rabawa shugaban jam’iyya N1m da nufin su ci abinci a Mr. Biggs domin samun yadda yake so.
7. Akpabio a majalisa yana Minista
Mr Akpabio yana minista aka gayyace shi majalisa bisa zargin cushen kwangilolin N500m a kasafin kudin hukumar NDDC a shekarar 2017.
Da ya je majalisar tarayyan, ministan na Neja Delta ya nemi tona asirin kowa, a karshe sai dai aka rika rokonsa ya yi shiru ya rufe bakinsa.
8. Shugaban majalisa ya yi zancen abinci
Ana da labari cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ba da shawara cewa ka da mutane su yi wasa da inda za a ci abinci kyauta.
Ganin ana cikin kuncin rayuwa a Najeriya, mutane sun caccake tsohon gwamnan na Akwa Ibom da cewa yana yi musu isgilanci ne ba komai ba.
'Dan majalisa ya fasa kwai
Sanata Ali Muhammad Ndume babban ‘dan siyasa ne, amma ana da rahoto cewa ya na ganin abokan aikinsa ba su da gaskiya ko kadan.
Sanatan na Borno (APC) ya yi wa ‘yan siyasa zindir, yake cewa sun yi kaurin-suna wajen satar kudi, ya ce kalilan ne suka fitta zakka a yau.
Asali: Legit.ng