Akpabio ya karbi wasu kwangilolin NDDC a lokacin ya na Majalisa - Nwoboshi
- A binciken da ake yi a hukumar NDDC an fara zargin Godswill Akpabio da laifi
- Peter Nwoboshi da Ministan su na rigima ne kan batun kwangiloli a Neja-Delta
- Sanatan ya ce Ministan kasar mai-ci ya karbi wasu kwangiloli a NDDC a 2017
Wasu sababbin bayanai su na fitowa a game da badakalar da ake zargin an tafka a karkashin hukumar NDDC da ke da alhakin kowa cigaba a yankin Neja-Delta a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban kwamitin Neja-Delta a majalisa, sanata Peter Nwaoboshi ya zargi ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio da aikata ba daidai ba.
Jaridar The Nation ta rahoto Peter Nwaoboshi ya fito ya na cewa Godswill Akpabio ya ki yin aikin kwangilar da ya samu a karkashin hukumar, kwangilar ta kai Naira miliyan 500.
Sanatan ya jefi ministan da wannan zargi mai nauyi ne daidai lokacin da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a binciki kudin da aka batar a NDDC.
KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka
Ministan na Neja-Delta, Akpabio ya karyata wadannan zargi, ya ce wasu ne kawai su ke gigin jawowa ma’aikatar ta sa bakin jini da kuma yunkurin bata masa suna a gwamnati.
A wani bincike da majalisar dattawa da wakilai ta ke yi game da barnar da aka tafka a NDDC, an gano akwai hannun Godswill Akpabio wanda tsohon gwamna ne a yankin kasar.
Peter Nwaoboshi ya ce Godswill Akpabio ya samu wasu kwangiloli a hukumar NDDC a shekarar 2017 lokacin ya na sanata a majalisa. Ya ce Akpabio bai yi wadannan ayyukan ba.
A wancan lokaci tsohon gwamnan ya bukaci a ba shi kwangiloli biyar na Naira miliyan 500 daga cikin kasafin kudin NDDC. Binciken majalisar ya ce ministan bai cika alkawari ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng