Zanga Zanga: Shettima Ya Kwantarwa Matasa Hankali, Ya Fadi Shirin Tinubu gare Su
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sha alwashin cigaba da tafiya da matasa a wannan gwamnati
- Kashim ya ce Bola Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da cigaban matasan Najeriya domin su dogara da kansu
- Legit Hausa ta yi magana da wani shugaban kungiyar matasa kan albishir da Kashim Shettima ya yi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana irin gata da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga matasa.
Kashim ya ce shugaban ya himmatu wurin tabbatar da taimakon matasa ta kowace hanya domin cigabansu.
Shettima ya fadi shirin Tinubu kan matasa
Shettima ya bayyana haka ne a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashim ya ce Tinubu yana mutunta matasa a zuciyarsa kuma yana sonsu duba da yadda ya ba su mukamai a gwamnatinsa.
Mataimakin shugaban kasar ya fadi haka yayin da ya karbi bakwancin shugabannin matasa na jam'iyyar APC a Abuja karkashin jagorancin Dayo Israel.
"Ina mai tabbatar muku da cewa Bola Tinubu ya damu da matasa duba da irin shirye-shiryensa gare su."
"Tinubu ya nuna hakan musamman a mukamai da kuma tsare-tsarensa da suka shafi matasa kai tsaye
- Kashim Shettima
Shettima ya yabawa matasa kan hakurinsu
Shettima ya ba da tabbacin kwarin guiwa kan gwamnatin Tinubu wurin samar da ababan more rayuwa a kasar.
Ya kuma yabawa matasan kan jajircewarsu da kuma hakuri inda ya ba su tabbacin biya musu bukatu idan sun taso
Legit Hausa ta yi magana da wani shugaban kungiyar matasa kan albishir da Kashim Shettima ya yi.
Kwamred Bashir Umar ya ce kowace gwamnati tana da tsare-tsarenta kan matasa amma matsalar ba yi isowa gare su.
Bashir ya ce babbar matsalar matasa yanzu rashin aikin yi ne da ilimi wanda ya ke tunzura su zuwa ga aikata laifuffuka.
Ya ce a tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari an yi wa matasa gata amma mafi yawan tsare-tsaren ba su yi nasara ba.
Kungiya ta gargadi gwamnan PDP kan Tinubu
Kun ji cewa wata kungiya a Arewacin Najeriya ta gargadi Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi kan kalamansa.
Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta yi gargadin ne bayan gwamnan ya yi shagube ga Bola Tinubu kan zaben 2027.
Asali: Legit.ng