Obasanjo Ya Gargadi Shugabanni, Ya Fadi Abin da Zai Samu Najeriya Nan Gaba

Obasanjo Ya Gargadi Shugabanni, Ya Fadi Abin da Zai Samu Najeriya Nan Gaba

  • Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi shugabanni a kasar nan kan matsalar da ke tunkaro wa
  • Dattijon ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta cigaba ba matukar shugabanni da 'yan kasa ba za su rungumi hakuri ba
  • Obasanjo ya ce akwai babbar barazanar kasar nan za ta rikice matukar jagorori ba su fara daukar ingantattun tsare-tsare ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi shugabanni da sauran 'yan Najeriya a kan su rungumi sulhu domin samar da ci gaba mai dorewa.

Cif Obasanjo ya fadi haka ne sa'ilin da ya karbi bakuncin yan majalisar wakilai guda shida da ke fafutukar samar da dokar wa'adi daya ga shugaban kasa na shekaru shida.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa ya aike da saƙon gaggawa ga Tinubu kan masu zanga zanga

Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya gargadi shugabanni a kan yiwa Najeriya kyakkyawan tanadi Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP
Asali: Getty Images

Punch News ta wallafa cewa tsohon shugaban wanda ya gana da 'yan majalisar a gidansa, ya ce akwai babbar matsala da ke tunkarowa idan ba a bi a hankali ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa nauyi ne babba ya rataya a wuyan shugabanni na yin adalci da samar da cigaba mai dorewa domin wanzuwar zaman lafiya.

"'Yan Najeriya na da dalilin zanga-zanga" - Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo ya ce 'yan Najeriya na da kwakkwaran dalilin gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati, Peoples Gazette ta wallafa.

"Yan Najeriya sun gaji, su na jin yunwa, ransu ya baci, ba su da aikin yi, wajibi ne a saurari bukatunsu," inji Obasanjo.

Ya ce ba wai sauya wa'adin mulki ko tsarin tafiyar da mulki kawai ake bukata a kasar ba, har da sauya yadda yan kasar da jagororinsu ke tafiyar da al'amuransu.

Kara karanta wannan

Bayan mayar da shi kotu, Ganduje ya fadi abin da za a yi wa bangaren shari'a

Obasanjo na ganawa da 'yan majalisa

A baya mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya shiga ganawar sirri da 'yan majalisa guda shida biyo bayan rincabewar abubuwa.

'Yan majalisar sun hada da Abdulmalik Danga daga Kogi, Dr Usman Midala daga Borno, Matthew Nwogu daga Imo, Peter Aniekwe Daga Anambra, Kama Nkemkanma daga Ebonyi, sai Ugochinyere Ikenga daga Imo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.