Bayan Mayar da Shi Kotu, Ganduje Ya Fadi Abin da Za a Yi wa Bangaren Shari'a

Bayan Mayar da Shi Kotu, Ganduje Ya Fadi Abin da Za a Yi wa Bangaren Shari'a

  • A daidai lokacin da gwamnatin Kano ta sake mayar da shugaban APC, Abdullahi Ganduje kotu, ya fadi hanyar taimakawa sashen shari'a
  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya bukaci yan siyasa su hada kai domin karfafawa bangaren shari'a wajen aiki yadda ya dace
  • Dakta Ganduje ta bayyana bukatar taimakawa sashen saboda muhimmin rawar da ya ke takawa wajen tabbatar da dimokuradiyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci 'yan siyasa kan muhimmancin cicciba sashen shari'a a kasar nan.

Dakta Ganduje, wanda gwamnatin Kano ke tuhumar gwamnatinsa da laifukan almundahana ya ce sashen shari'a na da muhimmanci wajen tabbatar da dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya gargadi shugabanni, ya fadi abin da zai samu Najeriya nan gaba

Dr. Amina Abdullahi Ganduje
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya nemi yan siyasa su hada hannu wajen inganta sashen shari'a Hoto: Dr. Amina Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa shugaban ya ce kamata ya yi jagororin siyasa su taimaka wa bangaren da abubuwan da ya ke bukata domin gudanar da aikinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce akwai kalubale a sashen shari'a

Shugaban APC na kasa, kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya gano wasu daga cikin matsalolin da su ka addabi bangaren shari'a.

Da ya ke jawabin yayin taron da majalisar bayar da shawara ga jam'iyyun siyasa (IPAC), Ganduje ya ce sai an hada hannu wajen magance matsalolin, Solace Base ta wallafa.

Wadanne matsaloli sashen shari'a ke fuskanta?

Tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana manyan kalubale guda uku da su ka addabi bangaren shari'a a kasar nan.

Ganduje ya ce daga cikin matsalolin akwai rashin isassun kudin gudanarwa, rashin sahihin yanci da jinkirin yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: abin da Ministan Tinubu ya fadawa Sanusi II da miyagu suka lalata cibiyar NCC

Ya ce amma hakan ba zai dakile muhimmin aikin da sashen ya yi na dabbaka dimokuradiyya ba.

Gwamnatin Kano za ta yi shari'a Ganduje

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta sake garzayawa kotu ta na tuhumar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da wawason kuɗin jama'a.

A wannan karon, gwamnatin Abba Kabir Yusuf na zargin Ganduje ya wawashe kudin kananan hukumomi da taimakon tsohon kwamishina, Murtala Sule Garo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.