Gwamna Ya Fadi Babban Darasin da Gwamnonin Arewa Suka Dauka daga Zanga Zangar Yunwa

Gwamna Ya Fadi Babban Darasin da Gwamnonin Arewa Suka Dauka daga Zanga Zangar Yunwa

  • Gwamnan jihar Nasarawa ya ce zanga-zangar yunwa ta farkar da gwamnonin Arewa daga barcin da suke yi, sun shirya daukar matakai
  • Alhaji Abdullahi Sule ya ce akwai bukatar gwamnonin Arewa su mayar da hankali kan magance matsalar yara masa zuwa makaranta
  • Gwamnan ya kuma koka kan yadda mafi yawan wadanda suka fita zanga-zanga a jiharsa almajirai ne inda ya fadi abin da ya kamata ayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce zanga-zangar yunwa da aka yi a Arewa kwanan nan 'zaburarwa ce' ga gwamnonin yankin.

Gwamna ya yi nuni da cewa akwai bukatar gwamnonin Arewa su tashi tsaye domin magance matsalar yara marasa zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

"Duk almajirai ne": Gwamna ya fadi wanene mafi yawan masu zanga zanga a Arewa

Gwamnan Nasarawa ya yi magana kan darasin da gwamnoni suka koya daga zanga zanga
Gwamna Sule ya ce zanga-zangar yunwa ta koyawa gwamnonin Arewa darasi. Hoto: @RealSlimRichie, @Harmless12345
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da gidan talabijin na Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya magantu kan zanga-zanga

A cewar Gwamna Sule:

“ Zanga-zangar da ake yi a Arewa kira ce ta 'mu farka' daga barcin da muke yi a matsayinmu na shugabanni. Yankin mu yana da kyau a harkar noma. Ya kamata kowa ya koma gona.
"Ga duk wanda ya san ni, ya san na kula da kamfanin sukari na Savannah. Ni ne sugaban dukkanin kamfanoni masu samar da sukari a Najeriya.
"Ina da ilimi sosai kan harkar noma, ina kaunar noma sosai, kuma ina ma da gonaki nawa na kaina. Muna da kadada 5,000 ta gona a Nasarawa, za mu fara noma a ciki."

"Almajirai ne masu zanga-zanga "- Gwamna

Gwamna Sule ya bayyana cewa mafi akasarin masu zanga-zanga a jiharsa Almajiri ne, wadanda ba su ma fahimci ma'anar zanga-zangar ba.

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

“A yayin zanga-zangar da ta gabata a Lafiya, yawancin wadanda suka fito kan titi almajirai ne. Wasu daga cikinsu ‘yan shekara biyar ne, wasu kuma shekara bakwai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan Nasarawa ya ce da yawa daga cikinsu ba su ma fahimci ma'anar zanga-zangar ba.

“Lokacin da muka matsa kan batun almajirai, wasu malaman addini sun soki lamarin. Amma daga abin da ke faruwa a yanzu babu wanda ke magana."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamnan Bauchi ya yi maganar zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnanBauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce zanga-zangar yunwa da ake yi a fadin kasar hannunka mai sanda ce ga gwamnonin Arewa.

Gwamna Bala Mohammed ya kuma caccaki jawabin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kan zanga-zanga, inda ya ce tsare-tsaren Tinubu ne suka jefa kasar a cikin mawuyacin hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.