Tinubu ya Ƙara Daukan Matakin Ragewa Talaka Raɗaɗin Cire Tallafin Man Fetur

Tinubu ya Ƙara Daukan Matakin Ragewa Talaka Raɗaɗin Cire Tallafin Man Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta kara motsawa domin ganin ta magance radadin cire tallafin fetur da ya jefa talakawa cikin wahalar rayuwa
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana ga shugaban kamfanin motocin Innoson domin samar da motocin CNG a Najeriya
  • Mista Innocent Chwuwuma ya yiwa yan Najeriya albishir bayan ganawarsa da shugaban kasa Bola Tinubu kan wahalar da ake sha

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kara cigaba da ƙoƙarin samar da motocin CNG domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da shugaban kamfanin motocin Innoson domin samar da motocin da gaggawa.

Kara karanta wannan

Betta Edu za ta koma kujerar minista? Tinubu ya yi muhimman sauye sauye a ma'aikatar jin ƙai

Bola Tinubu
Tinubu zai samar da motocin CNG daga kamfanin Innoson. Hoto: @cornelosigwe
Asali: Twitter

Legit tatttaro bayanai kan ganawar da Tinubu ya yi da Innoson ne a cikin sakon da jami'in yada labaran kamfanin ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mafita ga talaka kan cire tallafin fetur

Shugaban kamfanin motocin Innoson ya bayyana cewa samar da motocin CNG ne mafita ga wahalar da ake sha a Najeriya.

Legit ta ruwaito cewa ana sa ran cewa motocin CNG za su saukaka harkar sufuri a Najeriya kasancewar ba su aiki da man fetur.

Shugaban kamfanin ya ce duk wanda ya yi amfani da motocin zai tabbatar da cewa su ne mafita kuma talakawa za su shaida.

Yaushe za a samar da motocin CNG?

Innocent Chwuwuma bai ayyana lokacin da za su samar da motocin ba sai dai yace nan gaba kadan motocin CNG za su fara aiki a titunan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sake magana kan dawo da tallafin man fetur da kawo saukin abinci

Saboda haka Innocent Chwuwuma ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri da gwamnatin Bola Tinubu kan cewa sauki na zuwa a kusa.

A jiya Alhamis ne shugaban kamfanin ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa kan maganar samar da motocin.

Tinubu ya yi maganar tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi magana kan dawo da tallafin man fetur da yan Najeriya suka yi zanga zanga kwanan nan.

Ministan kudi, Wale Edun ne ya yi bayanin tare da faɗin kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa wajen shigo da tataccen man fetur a wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng