N57bn: Gwamnatin Kano Ta Sake Lafta Wasu Zarge Zarge kan Shugaban APC, Abdullahi Ganduje

N57bn: Gwamnatin Kano Ta Sake Lafta Wasu Zarge Zarge kan Shugaban APC, Abdullahi Ganduje

  • Tsuguno ba ta karewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba bayan gwamnatin Kano ta kara waiwayarsa
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sake maka Dr. Ganduje wanda tsohon gwamnan jihar ne har sau biyu kotu da zargin zamba
  • Ana zargin Abdullahi Ganduje da batar da Naira Biliyan 57 daga cikin asusun gwamnati da tallafin tsohon kwamishinansa, Murtala Sule Gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuma gurfanar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a gaban kotu bisa sabon zargi.

A sabuwar tuhumar, ana zargin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da tsohon kwamishinansa bisa zargin hada kai wajen almundahanar kudin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Abba Gida Gida ya ji koken jama'a, gwamna ya sa labule da 'yan kasuwa

Abba Kabir Yusuf
N57bn: An gurfanar da Abdullahi Ganduje kotu saboda cinye kudin kananan hukumomi Hoto: Abba Kabir Yusuf/Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ana zargin Dr. Ganduje, tsohon kwamishina Murtala Sule Garo da wasu mutum biyu da wawashe N57bn daga lalitar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Ganduje da almundahanar kananan hukumomi

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta zargi tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da wawashe kasafin da aka aikowa kananan hukumomi a zamaninsa.

Daily Post ta wallafa cewa an yi zargin Ganduje ya yi nasarar awon gaba da kudin ne da taimakon tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo.

Sauran wadanda gwamnatin ta maka kotu bisa zargin su na da hannu a cikin almundahanar su ne: Lamin Sani da Muhammad Takai.

An zargi Ganduje da tura kudin akawun

Gwamnatin Kano ta yi zargin tsohuwar gwamnatin Ganduje ta aika kudin jama'a akawun din daidaikun jami'an kudin kananan hukumomi.

Sannan an yi zargin sauya wasu daga cikin kudin zuwa Dala domin amfanin kashin kai. Premium Times ta ce za a kira shaidu 143.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya ware miliyoyi domin samar da ofisoshi ga masu ba shi shawara

Gurfanar da Ganduje gaban kotu a baya

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC na yanzu Abdullahi Umar Ganduje a kotu.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ce ta gurfanar da Ganduje, mai dakinsa Farfesa Hafsa Ganduje da dansa a gaban kotu bisa zargin handame kudin jama'ar jiha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.