“Duk Almajirai ne”: Gwamna Ya Fadi Wanene Mafi Yawan Masu Zanga Zanga a Arewa
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa ya bayyana takaici yadda 'yan yara masu karancin shekaru suka fito zanga-zanga
- Mai girma gwamnan ya ce mafi yawan wadanda suka fita zanga-zangar almajirai ne da ba su ma san dalilin hawa kan titunan ba
- Wannan martani na zuwa ne yayin da ake cigaba da zanga-zanga a fadin Najeriya kan halin matsi da tsadar rayuwa da ake ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nassarawa - Gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Sule ya bayyana damuwa kan yadda almajirai suka yi zanga-zanga
Gwamnan ya ce mafi yawan wadanda suka yi zanga-zangar matsin rayuwa a Arewacin kasar ba su san dalilin yin hakan ba.
Zanga-zanga: Gwamna Sule ya bukaci kawo sauyi
Gwamna Sule ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Alhamis 8 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule ya bayyana bukatar sake zama domin shawo kan matsalar almajiranci musamman a yankin Arewa.
Ya ce a shekarar 2020 sun yi zama tare kan matakin da za su dauka kan tsarin almajiri amma ba a yi nasara ba.
"Almajirai sun fi yawa a zanga-zanga" - Gwamna
"Lokacin da aka gudanar da zanga-zanga a Lafia, mafi yawan wadanda suka fito kan tituna almajirai ne."
"Yawancinsu ba su wuce shekara biyar da bakwai zuwa tara ba, kuma mafi yawansu ba su fahimci dalilin yin zanga-zangar ba."
"Da na yi magana da su daga baya ba su ma san musabbabin yin zanga-zangar tasu ba, dole mu zauna kan haka."
- Gwamna Sule Abdullahi
Gwamna Sule ya kushe masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya magantu bayan tabbatar da nasararsa da Kotun Kolin kasar ta yi.
Sule ya ce yan jihar su sani cewa duk irin zanga-zangar da zasu yi ba za ta sauya komai daga hukuncin da Kotun Kolin ta yanke ba.
Gwamnan ya bukaci su rungumi kaddara da kuma wanzar da zaman lafiya domin shi ne mafita gare su ba zanga-zanga ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng