NNPC ke Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa? Kyari Ya Wanke Kamfanin Najeriya
- Shugaban kamfanin na NNPC Limited, Mele Kyari ya ce kamfanin bai karya wata doka da ta ba da damar yin mu’amala da abokan huldar sa ba
- Kyari, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga kwamitin majalisar dattawa da ke binciken zagon kasa a masana’antar man Najeriya
- Shugaban NNPC ya kuma nemi da a nesanta kamfanin da shugabanninsa daga zargin sata ko yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari a ranar Laraba ya gurfana gaban kwamitin majalisar dattawa da ke bincike kan zagon kasa a fannin mai da iskar gas.
Mele Kyari, wanda ya yi bayani ga kwamitin majalisar bisa jagorancin Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce shugabannin NNPC ba barayi ko masu zagon kasa ba ne.
Majalisa ta yi taron kan harkar mai
Kafar labaran Arise News ta ruwaito masu ruwa da tsaki a harkar mai da gas sun amince a fallasa masu zagon kasa da ke kawo cikas a fannin ba tare da dagawa kowa kafa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka halarci taron kwamitin majalisar sun kuma amince da a watsa binciken da ake yi kai tsaye domin jama'a su ga yadda ake bincike kan lamarin.
Mahukunta daga kamfanin NNPC da kuma matatar man Dangote sun yi amfani da taron wajen yin karin haske kan rigimar da ta kaure tsakaninsu a kwanakin baya.
Kyari ya kare martabar kamfanin NNPC
Kamfanin NNPC ya nesanta kasansa daga zargin da ake yi masa na kawo cikas ga fara aikin matatar man Dangote, tare da yin zagon kasa ga tattalin arziki.
Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce "NNPC na biyayya da bin dokokin Najeriya," inda ya ce babu wata doka da kamfanin ya karya a mu'amalarsa da abokan huldarsa.
Kyari ya bayyana cewa sana’ar tace mai sana’a ce mai saukin kai wadda kowane mai saka jari ya kamata ya sani kafin ya shigo kasuwarta.
Wata sanarwar da babban jami’in sadarwa na NNPC, Olufemi Soneye ya fitar a shafin kamfanin na X, ta ruwaito Kyari na cewa:
“A kan zargin shigo da mai marar inganci, kamfanin NNPC Limited ba shi da wata alaka da hakan domin hukumomin da abin ya shafa ba za su amince da duk wani abin da bai dace ba.
“Muna masu dora yakini, biyayya da himma ga ci gaban kasar nan. Wajibi ne mu kare muradun wannan kasa mai girma gaba daya. Lallai ba mu karya wata doka ba."
"Yan majalisa sun nemi Kyari ya sauka
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan majalisar tarayya sun bukaci Mele Kyari ya yi murabus daga shugaban kamfanin NNPC.
'Yan majalisar sun ce an tafka barna a NNPCL karkashin Mele Kyari, kuma shi ne silar matsalolin da gwamnatin Bola Tinubu ke samu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng