Gwamna a Najeriya Ya Dage Takunkumi kan Basarake Mai Daraja Bayan Mummunan Zargi

Gwamna a Najeriya Ya Dage Takunkumi kan Basarake Mai Daraja Bayan Mummunan Zargi

  • Bayan dakatar da basarake na tsawon watanni shida a jihar Oyo, a yau Alhamis 8 ga watan Agustan 2024 ya dawo kan sarauta
  • Gwamnatin jihar ta dawo da basaraken na karamar hukumar Ido, Oba Gbolagade Babalola bayan kammala wa'adin da aka diba masa
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Seyi Makinde ya amince da dakatar da basaraken a ranar 2 ga watan Faburairun 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta janye takunkumin da ta kakaba kan wani fitaccen basarake a jihar bayan dakatar da shi na tsawon lokaci.

Gwamnatin jihar da janye dakatarwar ne kan basaraken na Ido, Oba Gbolagade Babalola bayan dakatar da shi na watanni shida.

Kara karanta wannan

Kowa ya rasa: Tinubu ya dakatar da siyar da shinkafar N40,000 ga 'yan Najeriya

Gwamna Makinde ya dawo da basarake bayan dakatar da shi
Gwamna Seyi Makinde a Oyo ya dage takunkumi kan basarake a jihar. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Twitter

TABLE OF CONTENTS

Basarake ya dawo kan kujerar sarauta

Shugaban karamar hukumar Ido, Sheriff Adeojo shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 8 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeojo ya bayyana haka ne yayin mika takardar dawo da basaraken inda ya taya shi murnar samun dawowa kan sarauta, Leadership ta tattaro.

Ya ce gwamnatin Seyi Makinde za ta cigaba da mutunta sarakunan gargajiya a matsayin masu wanzar da zaman lafiya.

Har ila yau, Adeojo ya yabawa Gwamna Makinde duba da yadda ya ke mutunta sarakunan gargajiya saboda muhimmancinsu.

Musabbabin dakatar da basaraken a Oyo

Wannan na zuwa ne bayan dakatar da basaraken a ranar 2 ga watan Faburairun 2024 kan zargin alaka da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Kwamishinan kananan hukumomi da kula da sarakunan gargajiya, Olusegun Olayiwola shi ya sanya hannu a takardar dakatarwar.

Kara karanta wannan

An samu baraka tsakanin shugaban Majalisar Tarayya da mataimakinsa? an gano gaskiya

Sarkin Kano ya shawarci 'yan zanga-zanga

Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci matasa kan bari ana amfani da su domin lalata rayuwarsu ta gobe

Sarkin ya nuna damuwa kan yadda matasa suka kai hari cibiyar NCC da ake shirin kaddamarwa a wannan mako da muke ciki

Sanusi II ya tura sakon jaje ga al'umma da gwamnatin jihar Kano da Gwamnatin Tarayya da kuma ma'aikatar sadarwa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.