PDP Ta Shirya Daukar Tinubu Aiki a Zaben 2027, Gwamna Ya Fadi Kuskuren Gwamnatin APC

PDP Ta Shirya Daukar Tinubu Aiki a Zaben 2027, Gwamna Ya Fadi Kuskuren Gwamnatin APC

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya koka da yadda tattalin arzikin kasar ya tabarbare inda ya ce gwamnatin APC ta gaza
  • Gwamnan Bauchi ya ce idan har lamura suka ci gaba da tafiya a haka to ba shakka PDP za ta ba Shugaba Tinubu aiki a zaben 2027
  • Gwamna Bala ya ce tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ya kawo sun kara jefa 'yan kasar a a mawuyacin hali wanda zai ba PDP nasara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce idan har Shugaba Bola Tinubu ya ci gaba da gudanar da mulki a haka, babu makawa PDP za ta lashe babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Gwamna ya feɗewa Tinubu gaskiya, ya faɗa masa halin da ya jefa ƴan Najeriya

Gwamna Bala ya ce a irin salon mulkin APC, to ba shakka zai gayyaci Shugaba Tinubu ya zama daraktan yakin zaben dan takarar shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa.

Gwamnan Bauchi ya yi magana kan gazawar gwamnatin Tinubu
Gwamnan Bauchi ya ce PDP za ta ba Tinubu daraktan yakin zabe a 2027. Hoto: @SenBalaMohammed, @officialABAT
Asali: Twitter

Gwamna ya ba Bola Tinubu shawara

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin kaddamar da yakin neman zaben PDP a zabukan kananan hukumomi na jihar Bauchi, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bala ya ce:

"Mutane na fama da yunwa, kuma suna cikin bacin rai. Matasa ba su da ayyukan yi, tsarin iliminmu ba ya aiki kuma tsare-tsaren gwamnati sun gaza fidda A'i daga rogo.
"Tsare tsaren da suka kawo ne suka jawo dukkanin wadannan matsalolin. A madadinku, ina sanar da Shugaba Tinubu ya canja tsare-tsarensa domin ba sa yin tasiri."

"PDP za ta ba Tinubu aiki" - Gwamna

Kara karanta wannan

"Zan gayyace ka zama daraktan kamfen PDP A 2027": Gwamna ya yi shagube ga Tinubu

Gwamnan na jihar da ke Arewa maso Yamma ya ci gaba da cewa:

"Idan har aka ci gaba da tafiya a haka, to a 2027 zan gayyaci Tinubu ya zama daraktan yakin zabenmu saboda ko ina PDP za ayi, kuma za mu ci zabe ba tare da wahala ba."

Wani bidiyo da Channels TV ta wallafa ya ruwaito Gwamna Bala ya nuna mamaki na inda dukkanin tallafin da gwamnatin tarayya ke rabawa suke makalewa.

"Na ji wasu ministoci na cewa an rabawa gwamnoni tireloli 70, an ba mu miliyan 500, shin nawa ita gwamnatin tarayya ke samu?
"Shi ya cire tallafin mai, a yanzu N30,000 ba za ta iya sai maka buhun masara ba. Albashi ba ya iya daukar dawainiyar mutane, duk wa ya jawo hakan?"

- Gwamnan ya tambaya.

Kalli bidiyon a kasa:

Gwamna ya caccaki manufofin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya ce manufofin shugaban kasa da jam’iyyar APC ne suka jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

Gwamnan ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya soke wasu daga cikin tsare-tsare da mnufofinsa domin tsamo mutane daga wahala ko kuma ya sha mamaki a zaben 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.