Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Boko Haram, Sun Wargazawa 'Yan Ta'adda Wajen Hada Bom

Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Boko Haram, Sun Wargazawa 'Yan Ta'adda Wajen Hada Bom

  • Rundunar sojin saman Nigeriya ta bayyana gagarumar nasarar da ta samu a yankin Arewa maso gabashin Najeriya
  • Sojojin Najeriya sun kai hari kan maboyar yan ta'addan Boko Haram bayan shafe lokaci mai tsawo suna farautar miyagun
  • Jami'in yada labaran rundunar sojin saman Nigeriya, AVM Edward Gabkwet ne ya sanar da haka a yau Alhamis a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojan saman Najeriya ta samu nasara kan yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Rahotanni na nuni da cewa sojojin sun yi ruwan bama bamai ne kan yan ta'addan tare da lalata musu wajen hada bom.

Sojojin Najeriya
Sojoji sun yi barin wuta kan Boko Haram. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'in yada labaran sojan saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet ne ya fitar da sanarwar.

Kara karanta wannan

An samu sabanin tsakanin 'yan sanda da rundunar sojoji a kan harbin 'yan zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asarar da sojoji suka yi wa Boko Haram

A yayin ruwan wuta da rundunar sojin saman Najeriya ta yi ga yan ta'addan Boko Haram ta wargaza inda yan ta'addan ke hada bom.

Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta kai harin ne kan yan ta'addan a yankin Grazah da ke Dutsen Mandara.

Rundunar sojin ta bayyana cewa ta shafe makonni tana kwanton ɓauna kan mafakar yan ta'addan kafin samun nasarar afka musu.

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa ta samu nasarar hallaka yan ta'addan Boko Haram a lokacin da ta musu luguden wutar.

Bayan haka rundunar ta kara tabbatar da cewa ta lalata manyan motocin sulke da yan ta'addar ke amfani da su yayin da ta sake musu wuta daga sama.

Punch ta ruwaito AVM Edward Gabkwet ya ce bayan sun sake wuta a wajen sun ga bakin hayaki ya mamaye sararin samaniya wanda hakan ke nuna sun lalata kayan yan ta'addar.

Kara karanta wannan

Daga ba jami'an tsaro shawara, Shugaban kasa Tinubu ya caccaki Atiku Abubakar

Sojoji sun harbi yaro a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojojin Najeriya ta cafke sojan da aka ce ya kashe wani karamin yaro dan shekara 16 a Samarun Zariya.

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa jami'in soja ya yi harbi a layin Sarkin Pawa da ke Samarun Zariya inda ya samu yaro a makogoro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng