Kowa Ya Rasa: Tinubu Ya Dakatar da Siyar da Shinkafar N40,000 ga ’Yan Najeriya

Kowa Ya Rasa: Tinubu Ya Dakatar da Siyar da Shinkafar N40,000 ga ’Yan Najeriya

  • Ana murna ma'aikata za su samu rangwame a shinkafar N40,000 da za a siyar, gwamnati ta dakatar da shirin a yau Alhamis
  • Gwamnatin ta fitar da sanarwa a yau Alhamis 8 ga watan Agustan 2024 inda ta ja kunnen daraktoci da manyan ma'aikata
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu ma'aikata sun fara rijistar neman cin gajiyar samun tallafin shinkarar a wannan mako da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin siyar da shinkafa mai nauyin kilo 50 ga 'yan Najeriya.

Tun farko gwamnatin ta so tallafawa ma'aikata ne domin samun shinkafar cikin farashi mai rahusa kan N40,000 kacal.

Kara karanta wannan

Izalah ta dauki mataki kan kuncin rayuwa, ta turawa limamai sako madadin zanga Zanga

Gwamnatin Tinubu ta fasa siyar da shinkafa mai nauyin kilo 50 kan N40,000
Gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da sanarwa game da dakatar da siyar da shinkafa kan N40,000. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamnati ta fasa saida shinkafar N40,000

Sakataren din-din-din na ma'aikatar ayyuka na musamman shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an dakatar da aka yada a ranar 1 ga watan Agustan 2024 ranar da aka fara zanga-zanga.

An bukaci duka daraktoci da shugabannin ma'aikatu da su sani an dakatar da shirin da aka yi domin ma'aikata, Punch ta tattaro.

Mene dalilin dakatar da saida shinkafar?

Sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana musabbabin dakatar da shirin ba bayan wasu daga cikin ma'aikata sun yi rijista.

"Ina mai sanar da ku wata sanarwa da aka fitar na ma'aikatar ayyuka na musammana ranar 1 ga watan Agustan 2024 da cewa na dakatar da wannan shiri.:
"Sauran bayanai za su biyo baya a lokacin da ya dace, ku sanar da duka wadanda suke karkashinku domin su san halin da ake ciki."

Kara karanta wannan

Dan Agundi ya kwantarwa matasa hankula, ya fadi gatan da Tinubu ya shirya musu

- Cewar sanarwar

Yadda za a ci gajiyar shinkafar N40,000

A baya kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta kammala shirin fara siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan N40,000 kacal a Najeriya.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne domin ragewa 'yan kasar halin kunci da suke ciki na mawuyacin hali a Najeriya.

An sanar da cewa ma'aikatan gwamnati ne kadai za su ci gajiyar shinkafar inda aka ba su sharudan cike ka'ida domin samun tallafin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.