Zanga Zanga: Birtaniya Ta Bayyana Halin da 'Yan Najeriya Mazauna Kasarta ke Ciki

Zanga Zanga: Birtaniya Ta Bayyana Halin da 'Yan Najeriya Mazauna Kasarta ke Ciki

  • Jakadan kasar Birtaniya a Najeriya, Dakta Richard Mongomery ya ce 'yan Najeriya mazauna kasar Turan na cikin koshin lafiya
  • Dakta Richard Mongomery ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana kan zanga-zangar da ta barke a wasu sassa na Birtaniya
  • A yayin da jakadan ya ba da tabbacin kula da 'yan Najeriya a Birtaniya, ya kuma fadi matakan da aka dauka domin dawo da zaman lafiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Birtaniya ta yi bayani kan halin da 'yan Najeriya mazauna kasarta suke ciki a yayin da zanga-zanga ta barke a wasu sassan kasar.

Babban jakadan Biritaniya a Najeriya, Dakta Richard Mongomery, ya ba da tabbacin cewa 'yan Najeriya za su samu tsaro a duk inda suke a kasar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

Birtaniya ta yiwa Najeriya karin haske kan zanga zangar da ake yi a kasarta
Birtaniya ta ba da tabbacin tsaron lafiya da rayukan 'yan Najeriya a lokacin zanga zanga. Hoto: @Worldsource24, @nidcom_gov
Asali: Twitter

Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Birtaniya

Dakta Richard ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Hon. Abike Dabiri-Erewa a Abuja, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun NiDCOM, Gabriel Odu ta fitar a ranar Laraba, Dakta Montgomery ya ce, garuruwa 12 ne zanga-zangar ta shafa.

Sai dai ya tabbatar wa al’ummar Najeriya mazauna Birtaniya cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin dawo da kwanciyar hankali a yankunan da abin ya shafa.

Birtaniya ta dauki mataki kan zanga zanga

Dakta Richard ya ce Birtaniya ta kafa kotuna na musamman guda 60 da suka hada da ‘yan sanda da jami’an shari’a na kasar domin magance tashe tashen hankulan.

Jakadan ya kara da cewa an kama sama da mutane 400 da ke da alaka da wannan tashin tashina, yana mai bayyana fatan cewa gwamnati Birtaniya za ta daidaita abubuwa nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Dan Agundi ya kwantarwa matasa hankula, ya fadi gatan da Tinubu ya shirya musu

Jaridar Tribune ta ruwaito Dakta Richart ya jaddada cewa Birtaniya za ta nemi adalci a kan wadanda ke kara ingiza masu zanga-zanga da kuma tunzura jama'a a yanar gizo.

Zanga-zanga: Sojoji sun karbi mulki a Bangladesh

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojoji sun sanar da karbar mulki a kasar Bangladesh bayan zanga-zangar adawa da rusa guraben ayyuka ta tsananta.

An ce Firaminista Sheikh Hasina ta yi murabus tare da tserewa zuwa Indiya domin neman mafaka yayin da masu zanga-zangar suka mamaye gidanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.