Jama'a Sun Dimauce da Wuta Ta Tashi a Gidan Mai Bayan Zanga Zanga Ta Lafa

Jama'a Sun Dimauce da Wuta Ta Tashi a Gidan Mai Bayan Zanga Zanga Ta Lafa

  • Masu sayen man fetur a jihar Legas sun shiga fargaba bayan wuta ta tashi a wani gidan mai ana tsaka da hada-hada
  • Wutar ta kama a gidan man mobil da ke kusa da Airport Hotel a titin Obafemi Awolowo a Ikeja, babban birnin Legas
  • An gano cewa wutar ta tashi da safiyar wannan Alhamis din amma ba a san musabbin ta ba har zuwa lokacin hada rahoton

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Jama'a sun shiga dimuwa bayan wuta ta tashi a gidan man Mobil da ke jihar Legas a safiyar ranar Alhamis lokacin jama'a su na shan mai.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta fitar da makudai a watanni 6, an batar da Naira tiriliyan 1

Gidan man da ke kusa da titin Airport Hotel a titin Obafemi Awolowo a yankin Ikeja da ke babban birnin Legas ya kama da wuta da karfe 10.49ns.

Lagos
Gobara ta kama a gidan man Mobil Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Wani mai amfani da shafin X, @Dub3m_aa ya wallafa bidiyon yadda wuta ta rika ci a gidan man yayin da jama'a ke ihun kowa ya yi ta kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai daukin kashe gobarar gidan mai

Jaridar Punch ta tattaro cewa an kai dauki gidan man Mobil da ke Legas bayan tashin wutar da ta daga hankalin masu shan mai a cikinta.

An gano masu kashe gobara da motocin kashe wuta a wajen su na ta kokarin shawo kan wutar bayan an samu rahoton bullar ta da kukan neman dauki.

A sakon da ta wallafa a shafinta na X, hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta nemi jama'a su kwantar da hankulansu, domin ma'aikata na aikin shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sake magana kan dawo da tallafin man fetur da kawo saukin abinci

Gobara ta kama kamfanin NNPCL

A wani labarin kun ji cewa an samu matsala a rijiyoyin mai mallakin kamfanin mai na kasa (NNPCL), amma an samu nasarar dakile wutar kafin ta yi gagarumar barna.

Hukumar kula da albarkatun mai ta NUPRC ya tabbatar da tashin gobarar, tare da bayyana cewa an dauki matakin kange wajen da ta tashi domin dakile afkuwar hakan a gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.