Zanga Zanga: Abin da Ministan Tinubu Ya Fadawa Sanusi II da Miyagu Suka Lalata Cibiyar NCC
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci matasa kan bari ana amfani da su domin lalata rayuwarsu ta gobe
- Sarkin ya nuna damuwa kan yadda matasa suka kai hari cibiyar NCC da ake shirin kaddamarwa a wannan mako
- Sanusi II ya tura sakon jaje ga al'umma da gwamnatin jihar Kano da Gwamnatin Tarayya da kuma ma'aikatar sadarwa.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuwa kan yadda matasa suka ruguza cibiyar NCC da ke jihar.
Sarkin ya bayyana kwarin guiwar cewa za a gyara cibiyar nan ba da jimawa ba saboda ya yi magana da Ministan Sadarwa, Bosun Tijani.
Sanusi II ya sake gargadin 'yan zanga-zanga
Hadimin gwamna Abba Kabir, Abdullahi Ibrahim shi ya wallafa faifan bidiyon ziyarar Sarkin a shafinsa na X a yau Alhamis 8 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya shawarci matasa da su yi karatun ta-natsu domin sanin makiyansu da kuma wadanda suke sonsu da cigaba.
"Ina farawa da mika jaje ga Gwamna da gwamnati da al'ummar jihar Kano da kuma Gwamnatin Tarayya da ma'aikatar sadarwa."
"Magana ta farko ga matasa a Kano ya kamata su bude idanunsu su fahimci masu sonsu da kinsu, an shirya wurin da za a samu matasa 3m domin koya musu aiki da na'ura mai kwakwalwa."
"Amma wadansu mutane madadin su fada muku ku koyi sana'a sai suka ba ku kudi ku zo ku kona wannan wuri."
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya fadi lokacin gyara cibiyar NCC
"A yau ya kamata a bude wannan wuri amma muka ji an kawo hari an kuma kona wannan wuri tare da sace kayan ciki."
"Mun yi magana da Ministan sadarwa ya bamu tabbacin za a gyara ko sake gina cibiyar NCC a kankanin lokaci."
Sanusi II
Sanusi II ya ja hankali kan zanga-zanga
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magan mai kama hankali kan shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya.
Sanusi II ya shawarci matasa da su guji shiga lamarin zanga-zangar da aka shirya ranar Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng