DSS Ta Warware Rudanin da Aka Shiga bayan Kai Samame Ofishin NLC Saboda Zanga Zanga

DSS Ta Warware Rudanin da Aka Shiga bayan Kai Samame Ofishin NLC Saboda Zanga Zanga

  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta warware rudanin da aka samu bayan kungiyar NLC ta zargeta da kai mata samame a tsakar dare
  • NLC ta ce jami'an hukumar DSS sun kutsa ginin hedikwatarsu da ke Abuja da misalin karfe 8 na dare inda suka kwashi littatafai da mujallu
  • Sai dai a wani martani da hukumar DSS ta fitar, ta bayyana cewa jami'anta ba su gudanar da wani aiki a ofishin kungiyar kwadagon ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta rahotannin da ke cewa jami’anta sun kai samame hedikwatar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"An yi wa gwamnatin Tinubu bakin tambari; Amnesty Int'l ta soki kutsen jami'an tsaro a ofishin NLC

Wannan musantawar na zuwa ne bayan zargin da NLC ta yi a ranar Laraba, na cewa hukumar ta aika da jami'anta dauke da makamai zuwa ofishinta, kuma sun kwashe wasu takardu.

DSS ta yi magana kan samamen da aka kai ofishin NLC na Abuja
DSS ta kare kanta bayan NLC ta zargeta da kai mata samame a tsakar dare. Hoto: @OfficialDSSNG, @NLCHeadquarters
Asali: Facebook

NLC ta zargi DSS da kai mata samame

A cewar wani rahoto na Channels TV, kungiyar NLC ta yi ikirarin cewa jami’an DSS sun mamaye ofishinta ne da misalin karfe 8:30 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun shiga suka yi watsa watsa da kantin sayar da littattafai a hawa na 2 inda suka kwashe daruruwan littattafai da wasu mujallu.
“Dakarun da suka kai samamen sun yi ikirarin cewa suna neman kayan da aka yi amfani da su wajen gudanar da zanga zangar adawa da gwamnati."

- Inji sanarwar da shugaban fannin yada labarai da hulda da jama’a na NLC, Benson Upah ya fitar.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame hedkwatar NLC bayan gano wani sirri kan zanga zanga

Jami'an DSS ne suka kaiwa NLC samame?

Sai dai a martanin da mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya ya mayar a ranar Alhamis, ya ce jami’anta ba su da alhakin kai samame ofishin NLC.

Sanarwar da Afunanya ya fitar wadda aka wallafa a shafin hukumar na X ta ce:

“Barka da safiya abokai. Don Allah a kula cewa hukumar (DSS) ba ta gudanar da wani aiki a ofishin NLC da ke Abuja ba.”

NLC ta yi wa DSS martani mai zafi

Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar NLC ta yi Allah wadai da farmakin da jami'an DSS suka kai ofishinta inda ta bukaci a gaggauta janye jami’an tsaron daga hedikwatar ta.

NLC ta ce jami’an tsaron da ke dauke da makamai ba su nuna wata takardar doka da ta ba su damar kutsawa hedikwatar kungiyar kwadagon a cikin dare ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.