An Yi Wa Gwamnatin Tinubu Bakin Tambari; Amnesty Int'l Ta Soki Kutsen Jami'an Tsaro a Ofishin NLC
- Yayin da aka wayi gari da labarin samamen da jami'an tsaro su ka kai babban ofishin kungiyar kwadago ta NLC, kungiyoyi sun fara raddi
- Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana samamen a matsayin karan tsaye ga hakkin 'yan kasar nan
- Shugaban kungiyar na Najeriya, Sanusi Isa ya bayyana cewa an kai samamen ne ba komai ba sai domin tsorata kungiyoyin kwadago
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty International ta caccaki hukumomin Najeriya bisa samamen da su ka kai ofishin kungiyar kwadago ta kasa.
A ranar Alhamis ne aka tashi da labarin jami'an tsaro na fararen kaya (DSS) sun kutsa babban ofishin kungiyar kwadago ta NLC da ke Abuja.
Jaridar Punch ta wallafa cewa a sanarwar da Amnesty Int'l ta fitar yau Alhamis, ta bayyana zargin jami'an sun dauki matakin domin cusa tsoro a zukatan jagororin kwadago a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin DSS ta kai samamen ne bisa zargin kungiyar kwadagon na da hannu wajen kitsa zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
"Akwai barazana ga NLC," Amnesty Int'l
Kungiyar hakkin bil adama ta Amnesty Int'l ta bayyana damuwa a kan tsaron rayukan shugabannin kungiyar kwadago ta NLC bayan jami'an DSS sun kutsa ofishinsu.
Sanusi Isa, wanda shi ne shugaban kungiyar na Najeriya ya bayyana kaduwa a kan yadda jami'an su ka yiwa doka karan tsaye wajen kai samamen.
Channels Television ta tattaro cewa kungiyar na zargin samamen wani shiryayyen hari ne a kan kwadago a kasar nan.
NLC ta yi martani kan kutsen DSS
A baya mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi Allah wadai da yadda jami'an 'yan sanda da na DSS su ka tirsasa shiga ofishinta a wani yunkuri na neman muhimman bayanai.
Sakataren kungiyar, Benson Upah ya ce wannan abin kunya ne matuka, ganin yadda ko a zamanin soja ba a yiwa hakkinta karen tsaye makamancin wanda aka gani a daren Laraba ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng