Gwamnatin Kano Za Ta Sa Kafar Wando Guda da Masu Lalata Gandun Daji, An Tsaida Hukunci

Gwamnatin Kano Za Ta Sa Kafar Wando Guda da Masu Lalata Gandun Daji, An Tsaida Hukunci

  • Gwamnatin Kano ta bayyana shirin kare gandun dajin da ke jihar da sauran dabbobin daji da ake da su domin inganta muhalli
  • Haka kuma gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samar da doka da za ka ba wadanda ke kula da gandun dajin Falgore kariya
  • Manajan daraktan gidan adana namun daji na Kano, Sadiq Kura Muhammad ya bayyana matsayar gwamnatin a dajin Falgore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta samar da dokar da za ta ba masu lura da gandun dajin Falgore a karamar hukumar Tudun Wada kariya.

Manajan daraktan gidan adana namun daji na Kano, Sadiq Kura Muhammad ne ya bayyana haka yayin bikin ranar masu kula da gandun daji na duniya.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Abba Gida Gida ya ji koken jama'a, gwamna ya sa labule da 'yan kasuwa

Kola Sulaimon
An kafa dokar kare dazuka a Kano Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin ta ce dokar za ta fara aiki kafin karshen 2024 domin hana masu kokarin lalata dazuka a jihar cimma burinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Sadiq Kura Muhammad ya kara da cewa daga cikin hukuncin da dokar ta tanada akwai daurin shekara 10 a gidan kaso.

Gwamnati za ta samar da ayyukan yi

Gwamnatin Kano ta dauki alkawarin samawa matasan Doguwa, Tudunwada da Sumaila ayyukan hannu domin rage lalata gandun dajin Falgore da ke kusa da su.

Manajan daraktan gidan adana namun daji na Kano, Sadiq Kura Muhammad ne ya bayyana haka a madadin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Gwamnati ta yi bikin ranar gandun daji

Gwamnatin Kano ta bi sahun takwarorinta na duniya wajen gudanar da bikin ranar girmama masu kare gandun daji.

A bikin da ya gudana a dajin Falgore, an bayyana yadda aka kashe akalla mutane 140 da ke kula da dazuka a kasashe 37.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya ware miliyoyi domin samar da ofisoshi ga masu ba shi shawara

Gwamnatin tarayya na shirin samar da aiki

A baya mun ruwaito yadda gwamnatin tarayya ta ba 'yan Najeriya hakuri, inda ta bayyana shirinta na samawa matasa miliyan daya ayyukan yi ta hukumar inganci da nagartar ayyuka.

Shugaban hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana shirin gwamnatin a daidai lokacin da matasa ke gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin Bola Ahmed Tinubu a kan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.