Kano: Mabarata Sun Shafe Kwanaki da Yunwa, Sun Nemi a Janye Zanga Zanga

Kano: Mabarata Sun Shafe Kwanaki da Yunwa, Sun Nemi a Janye Zanga Zanga

  • Yayin da aka shiga rana ta takwas ta zanga-zangar adawa da manufofin Bola Ahmed Tinubu, mabarata sun shiga jerin masu kokawa
  • Wasu daga cikin mabarata a jihar Kano sun bayyana cewa sai sun fito su ke samun abin kai wa bakinsu da na iyalansu
  • Amma zanga-zangar, wacce ta jawo dokar takaita zirga-zirga ta zamar masu karfen kafa, domin yanzu haka yunwa ce ke addabarsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wasu mabarata a Kano sun roki jagororin da su ka shirya zanga-zanga su yi hakuri, su janye saboda su samu damar fitowa neman na kai wa bakunansu.

Kara karanta wannan

"Ku amshi tayin gwamnati," Sarki ya lallashi masu zanga zanga

Mabaratan sun bayyana cewa kullum sai sun fito tituna neman na Annabi kafin su samu damar cin abinci ko ciyar da iyalansu da ke jiran su kawo masu abinci.

Pius Utomi Ekpei
Mabarata sun nemi a kawo karshen zanga-zanga Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa wani dattijo mai shekaru 70, Baba Halliru mazaunin Rijiyar Zaki ya ce su na gudanar da rayuwa cikin mawuyacin hali saboda ba sa iya fitowa bara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baba Halliru ya ce yau kwana biyu kenan babu wanda ya ci abincin kirki a cikin gidansa mai mutane 14 saboda ba su samu sadaka ba.

Zanga-zanga: Yadda mabarata ke zama da yunwa

Wasu daga cikin mabarata a jihar Kano sun tabbatar da kukan Baba Halliru na cewa yunwa za ta yi masu mummunar illa matukar aka cigaba da gudanar da zanga-zanga, Daily Post ta wallafa.

Malam Isa Musa da ke zama a Dorayi, karamar hukumar Kumbotso a jihar, ya roki gwamnati ta yi hobbasa wajen magance koken jama'a ko su ma za su samu saukin rayuwa.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun harzuka, za a gudanar da makokin wadanda aka kashe

"Mu na bara ne saboda ba mu da mai tallafa mana, tun bayan da aka sanya dokar takaita zirga-zirga ba mu samu mun ci abinci ba na kusan kwanaki uku," inji Malam Isa Musa.

Ganduje ya yi magana a kan zanga-zanga

A wani labarin kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnati na sane da halin matsin da ya sa 'yan Najeriya tsunduma zanga-zanga.

Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa jama'a su kara hakuri domin tsare-tsaren gwamnatin tarayya ke shirin aiwatarwa za su kawo karshen wahalar da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.