Hauhawar Farashi: Abba Gida Gida Ya Ji Koken Jama'a, Gwamna Ya Sa Labule da 'Yan Kasuwa
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya zauna da 'yan kasuwa domin lalubo hanyar magance hauhawar farashi
- Tun bayan fara zanga-zangar tsadar rayuka masu shaguna su ka kara farashin kayan masarufi, wanda su ka dora laifin a kan manyan yan kasuwa
- A zaman da aka yi ranar Laraba, an tattauna muhimman batutuwa da su ka jibinci sauko da farashin kayan da ci gaban tsaro a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta gayyaci kungiyar 'yan kasuwar jihar domin gano dalilin tsadar kayayyaki tun bayan fara zanga-zanga a ranar Alhamis.
Mazauna Kano sun koka bisa yadda aka samu tsadar kayayyaki, yayin da ake rasa wasu daga cikin kayan masarufi a shagunan cikin unguwanni.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa jama'a na shan wahala sosai, saboda haka ya kamata 'yan kasuwa su daidaita farashinsu,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya nusar da su a kan su da su ji tsoron Allah, su sassautawa jama'ar Kano ta hanyar rage farashi yadda ya kamata.
Abba Gida-Gida ya nemi hadin 'yan kasuwa
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hadin kan 'yan kasuwa wajen tsaftace kasuwanni a kokarin gwamnatinsa na tsaftace jihar Kano.
Gwamnan ya yi alkawarin sanya fitilun kan titi a kasuwar kwari domin karfafa harkar tsaro kamar yadda daraktan yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
'Yan kasuwa da gwamnatin Kano sun cimma matsayar ci gaba da hadin kai domin magance matsalolin da su ka addabi jihar.
Kano: Abba Gida-Gida zai yi manyan ayyuka
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 2.67 domin gudanar da manyan ayyuka a jihar, ciki har da samar da matsuguni ga ma'aikatar sufuri.
An amince da fitar da makudan kudin a zaman majalisar zartarwa da ya gudana ranar Talata, inda aka fitar da ₦164,949,693.46 domin sake gina shataletalen gidan gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng