Jami'an DSS Sun Kai Samame Hedkwatar NLC Bayan Gano Wani Sirri Kan Zanga Zanga
- Jami'an tsaro sun kai samame hedkwatar kungiyar kwadago ta kasa NLC a daren ranar Laraba kan zanga-zangar da ake yi a ƙasar nan
- Masu gadin wurin sun bayyana cewa jami'an sun rufe fuskokinsu a lokacin da suka shiga wurin kuma kai tsaye suka nufi ofishin shugaban NLC
- An ce jami'an na DSS sun ɗauki wannan matakin ne bisa zargin wasu ƴan kwadago da hannu a shirya zanga-zangar yunwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jami’an tsaro da ake kyautata zaton dakarun hukumar tsaron farin kaya watau DSS ne sun kai samame hedikwatar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.
Dakarun sun mamaye hedikwatar ne bisa zargin wasu ƴaƴan NLC da hannu a kitsawa da ɗaukar nauyun zanga-zangar da ake yi a faɗin kaar nan kan tsadar rayuwa.
Wasu shugabannin kwadagon da suka zanta da Daily Trust a daren Laraba, sun ce duk wanda ke cikin hedkwatar ya tafi gida a lokacin da jami’an tsaron suka shigo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda DSS ta kai samame hedikwatar NLC
Wani jagora a NLC ya ce ya kira daya daga cikin masu gadin da ke aiki ta wayar tarho inda ya tabbatar da cewa jami’ai rufe da fuskoki dauke da makamai sun afka wurin da misalin karfe 10 na dare.
Ya ce mai gadin ya shaida masa cewa jami’an sun wuce kai tsaye zuwa hawa na 10 inda ofishin shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero yake, Channels tv ta kawo labarin.
Jami’in ya kara da cewa mai gadin ya tabbatar masa cewa daga bisani jami’an da suka rufe fuska sun dawo hawa na biyu inda wasu ofisoshin kungiyar NLC suke.
Kungiyar NLC da DSS sun yi gum
Da aka tuntubi shugaban sashen yada labarai na NLC, Benson Upah, ya shaida wa ƴan jarida cewa nan ba da jimawa ba zasu fitar da sanarwa kan lamarin.
Duk wani ƙoƙari na jin ta bakin hukumar ƴan sandan farin kaya DSS ya ci tura, da aka kira mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya, bai ɗaga kiran ba.
Soja ya harbe matashi a Bauchi
Kuna da labarin rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa wani soja ya harbe matashi Habibu Aminu, har lahira a garin Lere da ke jihar Bauchi.
Lamarin ya auku ne a lokacin da sojoji suka yi arangama da matasa a Lere, ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa, wasu mutum shida sun jikkata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng