Bayan Kisan Yaro a Zaria, An Ji Labari Sojoji Sun Sake Harbe Matashi Har Lahira a Arewa

Bayan Kisan Yaro a Zaria, An Ji Labari Sojoji Sun Sake Harbe Matashi Har Lahira a Arewa

  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa wani soja ya harbe matashi Habibu Aminu, har lahira a garin Lere da ke jihar Bauchi
  • Lamarin ya auku ne a lokacin da sojoji suka yi arangama da matasa a Lere, ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa, wasu mutum shida sun jikkata
  • Kakakin rundunar ƴan sandan Bauchi ya ce tuni suka fara bincike domin gano sojan da ya yi wannan aika-aikata da kuma ɗaukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Bauchi ta tabbatar da cewa sojojin rundunar Operation Safe Haven sun kashe wani matashi mai suna Habibu Aminu a jihar.

Habibu ya rasa rayuwarsa ne a lokacin wata arangama tsakanin dakarun sojojin da kuma matasa a garin Lere da ke ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata da kisan ɗan uwansu, sun bankawa fadar basarake wuta a Arewa

Sufetan yan sanda na kasa, IGP Kayode.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kisan wani matashi a Bauchi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Daily Trust ta tatttaro cewa ganau sun bayyana cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu shida suka raunata a lokacin da sojoji suka shiga gidajen masu hannu a lamarin a Lere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun ƴan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami'an sun fara bincike domin gano abin da ya afku.

Yadda matasa suka yi arangama da sojoji

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da 'yan jam'iyyar PDP daga garin Lere suka yi arangama da dakarun sojojin rundunar Operation Save Haven da ke Tafawa Ɓalewa.

A ruwayar Leadership, SP Ahmed Wakil ya ce:

"Ƴan sanda sun kai ɗaukin gaggawa bayan samun labari kuma kwamishinan ƴan sandan Bauchi, Auwal Musa Mohammed ya tura ƙarin dakaru domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame hedkwatar NLC bayan gano wani sirri kan zanga zanga

"Bugu da ƙari an kafa tawaga ta musamman domin gudanar da bincike mai zurfi domin a yiwa kowa adalci, za a kama jami'an da ke da hannu kuma doka za ta yi aiki a kansu."

Bala Mohammed ya soki jawabin Tinubu

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya caccaki jawabin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan zanga-zangar da ake yi

Ƙauran Bauchi ya ce gaba ɗaya jawabin shugaban ƙasar bai da wata ma'ana ko matakin warware tsadar rayuwar da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262