Ana Daga Tutar Rasha, Amurka da Birtaniya Sun Fadi Matsaya kan Manufofin Tinubu
- Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a Najeriya, gwamnatocin Amurka da Burtaniya sun yi martani kan halin da ake ciki
- Kasashen biyu sun tura sakon jaje ga wadanda suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da aka kwashe kwanaki bakwai ana yi
- Wannan martani na kasashen na zuwa ne yayin da ake zanga-zanga a Najeriya kan halin matsi da kuma tabarbarewar tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatocin Amurka da Burtaniya sun yi magana kan zanga-zanga da ake yi a Najeriya.
Duka kasashen biyu sun yaba da tsare-tsaren Bola Tinubu musamman a fannin tattalin arziki.
Martanin Amurka da Burtaniya kan zanga-zanga
Wannan na kunshe a cikin sanarwa da kasashen suka fitar mabambanta a yau Laraba 7 ga watan Agustan 2024, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasashen sun bukaci shugaban ya cigaba da neman hanyar tattaunawa da masu zanga-zangar domin shawo kan matsalar, Punch ta tattaro.
Jakadan Burtaniya a Najeriya, Richard Montgomery da na Amurka, Richard Mills sun yabawa jami'an tsaro yadda suka gudanar da zanga-zangar.
Zanga-zanga: Kasashen biyu sun yabawa tsare-tsaren Tinubu
Mills a bangarensa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu ko tafka asara ta kowane hali yayin da ake zanga-zangar.
Ya ce tsare-tsaren Tinubu sun zama dole kuma Amurka tana goyon baya domin tabbatar da bunkasar tattalin arziki a Najeriya.
Montgomery shi kuma ya yabawa jami'an tsaro kan yadda ba su yi amfani da karfi ba kan matasa da ke zanga-zanga.
Ya ce sun san yadda Gwamnatin Najeriya ta himmatu wurin tabbatar da an gudanar da zanga-zangar cikin lumana.
Dalilin Tinubu na kin dawo da tallafi
A wani labarin, kun ji cewa Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun ya yi magana kan dalilin da ya sa Bola Tinubu ba zai dawo da tallafin mai ba.
Wale Edun ya ce babu kason tallafin mai a cikin kasafin da Tinubu ya mika a Majalisar Tarayya na wannan shekara ta 2024.
Martanin na zuwa ne yayin da masu zanga-zanga ke bukatar shugaban ya dawo da tallafin man fetur kamar yadda ya cire.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng