Zanga Zanga: Sanusi II Ya Fadi Masu Laifi kan Barnar da Aka Yi a Kano, Ya Yi Addu’a
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya koka kan rawar da jami'an tsaro suka taka kafin faruwar zanga-zanga a jihar
- Sarkin ya ce tun kafin faruwar hakan an rubutawa jami'an tsaro domin daukar mataki amma suka yi sakaci har aka yi barna
- Sanusi II ya koka kan yadda aka lalata dukiyoyi da kuma rasa rayukan al'umma inda ya ce barnar da aka yi shiryawa aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan zanga-zanga da ake cigaba da yi musamman a jihar.
Sarkin Kano ya bayyana cewa rashin daukar matakan da ya dace da sakacin jam'ian tsaro ne ya jawo rasa rayuka da dukiyoyi.
Muhammadu Sanusi II ya magantu kan zanga-zanga
Sanusi II ya bayyana haka ne yayin ziyara a cibiyar NCC Digitar Park da sauran wurare da aka farfasa a jihar, cewa Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basaraken ya ce an sanar da jam'ian tsaro kan lamarin amma ba su dauki matakin da ya dace ba har aka kaddamar da harin kan dukiyoyi.
Ya ce duk wadanda suka yi barna a jihar makiya Kano ne kuma daman an riga an shirya hakan duk wanda ya lura zai gane.
Zanga-zanga: Sanusi II ya ce akwai hannun makiya
"Abin da muke fada ne, duk mai hanu a wannan lamari makiyin Kano ne da mutanenta, abin da ya faru a Kano shiryawa aka yi."
"Ana son rusa jihar Kano amma muna addu'ar Allah ya hana su samun nasara muna rokon Ubangiji ya mayar da mafi alheri."
"Kafin faruwar haka an fadawa jam'ian tsaro a rubuce madadin kare faruwar hakan amma suka bari aka aikata barna, duk mai hannu a ciki zai ga sakamakonsa."
- Muhammadu Sanusi II
Sarkin daga bisani ya yi addu'ar Allah ya ba gwamnati damar dawo da abin da jihar ta rasa inda ya ce matasa suna bukatar addu'a sosai.
Sanusi II ya gargadi matasa kan zanga-zanga
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magan mai kama hankali kan shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya.
Sanusi II ya shawarci matasa da su guji shiga lamarin zanga-zangar da aka shirya fita gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng