An Samu Sabani Tsakanin 'Yan Sanda da Rundunar Sojoji a kan Harbin 'Yan Zanga Zanga
- Bayan babban Sufeton 'yan sandan kasar nan, Kayode Egbetokun ya karyata rahotannin cewa jami'ansu sun harbi masu zanga-zanga
- Rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da cewa jami'an tsaro sun bude wuta a kan jama'a masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati
- Daraktan yada labaran rundunar, Onyeama Nwachukwu ya bayyana cewa harbin ne ma ya yi sanadin rasuwar matashi mai shekaru 16 a Zariya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - An samu bambancin furuci tsakanin hukumomin tsaron kasar nan a kan harba bindiga yayin zanga-zangar lumana da matasan kasar nan ke gudanarwar.
Tun a ranar Alhamis da aka fara gudanar da zanga-zangar aka ji harbin bindiga a wasu jihohin kasar nan kamar Kano da Legas.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa amma babban sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ya fito bainar jama'a ya na cewa babu jami'insu da ya harbi matasan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun karyata Sufetan yan sanda
Gabanin rundunar sojojin kasar nan ta bayyana cewa an yi harbi har ya jawo asarar rai a Zariya, an samu rahotannin wuraren da aka ji harbe-harbe.
Punch News ta wallafa cewa rundunar ta tabbatar da cewa jami'inta ne ya halaka matashi mai shekaru 16 a Samaru.
Wuraren da aka ji harbe-harbe lokacin zanga-zanga
An ji karar bindiga a jihar Neja inda aka yi zargin harbin mutum shida, sai kuma a Kubwa, Abuja da fargabar kashe matashi guda.
Rahotannin harbe-harbe sun sun bulla a Bauchi, Kano, Jigawa, Katsina da Borno har da fargabar rasa rayuka.
Kisan matashi: Rundunar soja za ta yi hukunci
A baya kun ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta bayyana takaici da alhini bisa yadda jami'inta ya halaka matashi mai shekaru 16 a Samaru, Kaduna.
Daraktan yada labaran rundunar, Manjo janar Onyeama Nwachukwu ya tabbatar da kisan, sannan ya ce an kama bankin da ake zargi domin ladabtarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng