Mulkin Soja: Hamza Al Mustapha Ya Tura Sakon Musamman Zuwa ga Yan Najeriya

Mulkin Soja: Hamza Al Mustapha Ya Tura Sakon Musamman Zuwa ga Yan Najeriya

  • Tsohon mai tsaron Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi bayani kan mulkin soja da wasu ke ribibi a yau
  • Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi tsokaci kan masu daga tutar kasar Rasha yayin zanga zangar tsadar rayuwa a Najeriya
  • Legit ta tattauna da wani matashi mai fatan mulkin soja, Hamza Tukur kan maganar da Manjo Al-Mustapha ya fada

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai tsaron tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi bayani ga yan Najeriya kan mulkin soja.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya fadi rawar da ya kamata sojoji su taka a lokacin mulkin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Birtaniya ta bayyana halin da 'yan Najeriya mazauna kasarta ke ciki

Almustpha
Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi magana kan mulkin soja. Hoto: Hamza Al-Mustapha, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Al-Mustapha ya yi magana ne bayan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al-Mustapha: 'Babu mafita cikin mulkin soja'

Vanguard ta wallafa cewa Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce ya fahimci cewa yan Najeriya masu kiran mulkin soja a fusace suke.

Sai dai duk da haka ya bayyana cewa mukin soja ba shi ne mafita ga halin da yan Najeriya ke ciki ba.

'Akwai gyara a Najeriya.' - Al-Mustapha

Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce yadda yan Najeriya ke kira ga mulkin soja ya nuna cewa akwai bukatar shugabanni su sake zama domin magance matsalolin ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa sojoji ya kamata su zamo masu tallafawa dimokuraɗiyya ne da samar da tsaro a kasa.

Maganar Al-Mustapha kan tutar Rasha

Har ila yau, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce masu daga tutar Rasha ba lallai ya kasance suna kiran kasar ta shigo Najeriya ba ne.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban CDD ya ragargaji Tinubu, Farfesa ya fadi abin da ya fusata talaka

Sai dai ya ce hakan na nuna cewa mutane suna cikin kunci kuma suna neman mafita kan halin da suke ciki.

Legit ta ttauna da Hamza Tukur

Hamza Tukur ya zantawa Legit cewa lallai abin da Manjo Hamza Al-Mustapha ya fada ya kama hankalinsa.

Matashin ya ce ko ba komai Al-Mustapha ya san yadda mulkin soja ya kasance kuma ya koma kan ra'ayinsa a halin yanzu.

APC ta yi zargin juyin mulki

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya domin fara nuna sabon salon goyon baya ga shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohi, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana lamarin a birnin tarayya Abuja domin kare Tinubu daga zargin juyin mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng