Dan Agundi Ya Kwantarwa Matasa Hankula, Ya Fadi Gatan da Tinubu Ya Shirya Musu
- Babban daraktan hukumar NPC, Baffa Dan Agundi ya bayyana shirin ma'aikatarsa wurin samar da ayyukan yi a Najeriya
- Dan Agundi ya ce idan Bola Tinubu ya amince da shirin hakan zai samar da ayyukan yi har miliyan daya ga 'yan kasar
- Ya ce bayan ribar samar da aikin yi kuma shirin zai rika kawowa gwamnatin N3bn kowane wata kudin shiga domin wasu ayyukan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban hukumar inganci da nagartar ayyuka ta NPC ya yiwa matasan Najeriya albishir ana tsaka da zanga-zanga.
Baffa Dan Agundi ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya samar da ayyuka miliyan daya ga 'yan kasar.
Dan Agundi ya yi albishir ga matasa
Dan Agundi ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Laraba 7 ga watan Agustan 2024, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan hukumar NPC ya ce ma'aikatarsa ta fara zantawa da Ministan kwadago da samar da aikin yi domin tabbatar da shirin.
Ya idan har shirin ya samu sahalewar Bola Tinubu zai samar da aikin yi da kuma kawo kudin shiga N3bn kowane wata ga gwamnatin.
"Alherin da ke cikin shirin" - Dan Agundi
"Wannan shirin zai samar da ayyuka miliyan daya ga 'yan Najeriya da za su rika samun N150,000 a matsayin albashi a mataki na shida na aikin gwamnati."
"Mun shirya hakan ne domin goyon baya ga kudirin Shugaba Bola Tinubu wurin samar da aikin yi da kawar da yunwa a kasa."
"Idan har Tinubu ya amince da shirin tare da hadin guiwar gwamnoni, Najeriya za ta dawo kan ganiyarta saboda za mu samu wadataccen abinci da ayyukan yi."
- Baffa an Agundi
Aminu Ado ya taya Dan Agundi murna
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi martani bayan nada Baffa Dan Agundi mukami a Najeriya.
Aminu Ado ya taya Dan Agundi murnar samun mukamin shugaban hukumar inganci da nagartar ayyuka ta NPC.
Tsohon sarkin ya taya Dan Agundi murnar bayan ya kiransa wayar salula inda ya yi masa fatan alheri da yi masa gargadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng