Masu Zanga Zanga Sun Harzuka, Za a Gudanar da Makokin Wadanda Aka Kashe
- Bayan an samu mutuwar wasu daga cikin masu zanga-zanga a fadin Najeriya, jagororin tattakin sun sanya ranakun makoki
- Wannan na kunshe cikin sanarwar da Hassan Soweto, Ayoyinka Oni da Adegboyega Adeniji su ka sanyawa hannu
- An samu akasi bayan wasu daga cikin masu zanga-zangar sun rasa rayukansu a lokacin da jami'an tsaro su ka bude masu wuta
. A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas - Masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun koka bisa yadda jami'an tsaro su ka kashe wasu daga cikinsu.
An samu rahoton kisan wasu daga cikin masu zanga-zanga da matasa 'yan ba ruwana a jihohin Kano, Kaduna da Katsina.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Hassan Soweto, Ayoyinka Oni da Adegboyega Adeniji ne su ka sanya hannu a kan sanarwar makokin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ce dole ne su nuna alhini a kan yadda jami'an tsaro su ka rika kashe su saboda sun fito neman a saukaka masu halin da kasa ke ciki.
Za a yi makokin kwanaki 3
Mutanen da su ke jagorantar zanga-zanga a jihar Legas sun fitar da tsarin yadda za a yi makokin mutanen da jami'an tsaro su ka kashe a kasar nan.
Jaridar Guardian ta wallafa cewa masu zanga-zangar sun dauki matakin nuna alhininsu a fili tun da gwamnatin Legas da 'yan sanda sun ki ba su kariya.
Za a gudanar da makokin daga Laraba zuwa Juma'a ta hanyar gudanar da taro ta shafin X, sannan a ɗora da tattakin rike kyandir a jihar.
An shiga makoki a Kaduna
A baya mun ruwaito yadda wani jami'in rundunar sojojin kasar nan ya jefa mazauna yankin Samaru a cikin takaici bayan ya harbe wani matashi.
Bayanai sun nuna cewa sojojin sun bude wuta a lokacin da su ka shiga Unguwar Pawa wanda ya sa kowa shiga, amma wani soja ya harbi kofar gidan yaron har ya rasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng