Gwamnan Kano Ya Ware Miliyoyi domin Samar da Ofisoshi ga Masu Ba Shi Shawara

Gwamnan Kano Ya Ware Miliyoyi domin Samar da Ofisoshi ga Masu Ba Shi Shawara

  • Gwamnatin Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin yin wasu ayyuka da ta ambata a jihar
  • Daga cikin ayyukan da gwamnatin za ta yi, ta ambaci samar da ofis ofis ga masu taimakawa gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Gwamnatin jihar ta bayyana dalilan samar da ofisoshin ga jami'an gwamnan a wannan lokacin da kudin da aikin zai laƙume

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin gina ofisoshi ga wasu jami'an gwamnatin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ware kudin ne yayin da zaman majalisar gwamnatin jihar na 17 ya gudana a fadar gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, Abba ya dauko muhimman ayyuka 7 domin farfaɗo da Kano

Gwamna Abba
Gwamnatin Kano za ta gina ofisoshi ga ma'aikata. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan kudin da gwamnan zai kashe ne a cikin sakon da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gina ofis a Kano: Nawa za a kashe?

Yayin zaman majalisar gwamnatin Kano, Abba ya amince da ware kudi sama da N268m domin samar da ofisoshin gwamnati.

Sanusi Bature ya wallafa cewa za a samar da ofisoshin ne a jikin baban dakin karatun jihar inda za a mayar da sashensa wurin aiki.

Su wa za a samarwa ofishin a Kano?

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa za a samar da ofisoshin ne ga masu ba gwamnan shawara na musamman.

Haka zalika gwamnatin ta bayyana cewa ma'aikatar sufuri ta jihar Kano za ta samu ofisoshi a wajen.

Amfanin ofisoshin da za a yi a Kano

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnatin Abba Gida Gida ta amince da fitar da N2.67bn domin manyan ayyuka

Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya bayyana cewa za a samar da ofisoshin ne domin wadatar da ma'ikata da wuraren aikin zamani masu inganci.

Samar da ofisoshin na cikin ayyuka da dama da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki damarar yi a zamanta na 17 da ta yi a fadar gwamnatin jihar.

Kano: Yan Kannywood sun koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa ana kara samun yan jam'iyyar NNPP a jihar Kano su na cigaba da sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai mulki a Najeriya.

An samu wasu fitattun jaruman Kannywood sun kara ficewa daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf suka koma APC ta hannun Sanata Barau Jibrin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng