Allah Ya tona asirin Limamin da ya shirya damfarar mabiyansa N3,000,000

Allah Ya tona asirin Limamin da ya shirya damfarar mabiyansa N3,000,000

Wani babban limamin cocin Methodist dake garin Ado-Ekiti na jahar Ekiti ya shiga hannun jami’an rundunar Yansanda bayan shirinsa na yin garkuwa da kansa tare da neman kudin fansa naira miliyan uku daga mabiyansa bai yi nasara ba.

Legit.ng ta ruwaito Limamin mai suna Adewuyi Adegoke ya hada baki ne da wani mutumi Oluwadare Sunday wanda ya turashi ya amso naira miliyan uku daga wajen mabiyansa domin a sako musu Limaminsu da suke zaton an yi garkuwa dashi.

KU KARANTA: Ana tare: Shehi Dahiru Usman Bauchi ya goga gemu da gemu da Sarkin Kano (Hotuna)

Allah Ya tona asirin Limamin da ya shirya damfarar mabiyansa N3,000,000
Allah Ya tona asirin Limamin da ya shirya damfarar mabiyansa N3,000,000
Asali: Facebook

A ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni ne Limamin ya boye a gida, amma sai ya aika da rahoto ga mabiyansa wai cewa yan bindiga sun yi garkuwa dashi a tsakanin garin Esa-Oke na jahar Osun da garin Aramoko na jahar Ekiti.

Daga bisani sai abokan aikinsa suka kira mabiyan Faston suna barazanar kasheshi idan har basu biya kudin fansan ba zuwa ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, nan da nan mabiyansa suka shiga kafafen sadarwar zamani suna nema masa taimako.

Guda daga cikinsu ma cewa yayi: “Jama’a ku taimaka mu tara kudi domin ceto wannan bawan Allah.” Sai dai Yansanda sun samu nasarar cafke dan aiken Faston, Sunday, a lokacin da ya tafi karban kudin fansan.

Daga nan karyar Fasto ta kare, saboda kai tsaye Sunday ya jagoranci Yansanda zuwa Otal din da Faston ya buya, anan Yansanda suka yi ram dashi, sa’annan suka tasa keyarsa zuwa babban ofishinsu dake garin Ado Ekiti.

Kwamishinan Yansandan jahar Amba Asuquo ya tabbatar da lamarin, kuma ya yi alkawarin fitar da cikakkiyar bayani dangane da bahallatsar da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel