Aminu Ado Ya Ci Karo da Cikas da Ɗan Uwansa Ya Yi Mubaya'a ga Sanusi II a Bidiyo
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na cigaba da samun cikas a kokarin neman dawowa kan karagar sarautar jihar bayan tuge shi da aka yi
- Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da dan uwan tubabben Sarkin, Ahmad Ado Bayero ya kai fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jihar
- A baya, hakimai da dagatai da wasu malaman addinin Musulunci sun kai ziyara fadar Sarkin domin yin mubaya'a gare shi da nuna goyon baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Duk da cigaba da zanga-zanga da ake yi a fadin Najeriya, Sarki Muhammadu Sanusi II na karbar baki.
Wasu daga cikin na hannun daman Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun kai ziyara fadar Sarki Muhammadu Sanusi II.
Dan'uwan Aminu Ado ya ziyarci Sanusi II
A cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X an gano Ahmad Ado Bayero a fadar yayin ziyarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon an gano ɗan uwan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado ya kai ziyara domin yin mubaya'a ga Sarkin a fadarsa.
Ahmad Ado Bayero wanda shi ne tsohon shugaban ma'aikatan tubaɓɓen Sarkin kuma Sarkin Dawaki Tsakar Gida ya nuna goyon baya ga Sanusi II.
Kano: Aminu Ado ya kalubalanci tsige shi
Hakan na zuwa ne yayin da aka shafe makwanni ana rigimar sarautar Kano kafin fara zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agustan 2024.
Tun bayan tuge Aminu Ado daga sarautar jihar da Gwamna Abba Kabir ya yi, Sarkin na 15 ya shiga kotu domin kwatar hakkinsa na cin mutunci da zarafi.
Sanusi II ya gargadi masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan masu shirin fara zanga-zanga musamman a jihar.
Sanusi II ya shawarci matasa musamman a jihar da kada su kuskura su bari a yi amfani da su wurin ruguza kasar Najeriya.
Wannan gargadi na Muhammadu Sanusi II ya ba da shi ne kwanaki kafin fara zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agustan 2024 da muke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng