Kano: An Kama Ƴan Kasar Waje da ke Ɗaukar Nauyin Ɗaga Tutocin Rasha, Bayanai Sun Fito

Kano: An Kama Ƴan Kasar Waje da ke Ɗaukar Nauyin Ɗaga Tutocin Rasha, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta sanar da cafke wasu ‘yan kasar waje da ake zargi da shirya zanga-zangar adawa da yunwa a jihar
  • Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Salman Dogo ya bayyana hakan biyo bayan wata ganawar tsaro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi da shi
  • A cewar kwamishinan ‘yan sandan, an kama mutanen ne bayan da aka tsananta bincike yayin da ya gargadi masu son tada husuma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana kame wasu ‘yan kasar waje da ake zargi da daukar nauyin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da aka yi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Salman Dogo ne ya sanar da hakan biyo bayan ganawarsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Talata 6 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

"Mun tsaurara matakan tsaro," Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita

'Yan sanda sun yi magana kan kama 'yan kasar waje masu hannu a zanga-zangar Kano
‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan kasar waje da ke daukar nauyin daga tutar kasar Rasha a Kano.
Asali: Facebook

Masu zanga-zanga suna daga tutocin Rasha

Kamar yadda jaridar The Cable ya ruwaito, an ga masu zanga-zanga a Kano suna daga tutocin kasashen waje, musamman tutocin Rasha, inda suke kira ga Shugaba Vladimir Putin da ya sa baki a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin daga tutocin Rasha ya bazu zuwa wasu garuruwan Arewacin kasar nan da suka hada da Jos, Kaduna, da Abuja, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin hukumomin tsaro.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan, an kama mutanen ne bayan da aka tsananta bincike, inda ya yi gargadin cewa za a gurfanar da duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga tsaron jihar.

'Yan sandan Kano na kokarin tabbatar da tsaro

Salman Dogo ya bayyana cewa, hukumomi na daukar matakan da suka dace domin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar, ciki har da sassauta dokar hana fita, inji rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Matasan jiha sun janye zanga zanga, sun bayyana matakin da za su ɗauka

Shugaban hafsan tsaron kasar, Christopher Musa, ya yi gargadin cewa daga tutocin kasashen waje a yayin zanga-zangar cin amanar kasa ne.

Gargadin Christopher Musa ya zo ne bayan taron tsaro na kasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta.

Daga tutar rasha: An fallasa 'yan siyasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaro sun fara bincikar wasu 'yan siyasar Arewa bisa zarginsu da daukar nauyin zanga-zanga da daga tutar Rasha a shiyyar.

Rahoto ya nuna cewa 'yan siyasar dai sun fito ne daga jihohin Katsina, Kaduna da Kano, kuma sun taka rawa mai girma a zaben 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.