Bayan Zanga Zanga, Abba Ya Dauko Muhimman Ayyuka 7 Domin Farfaɗo da Kano
- Gwamnatin Kano ta dauki aniyar fara manyan ayyuka da za su laƙume makudan kudi domin kawo cigaban zamani a jihar
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ayyukan za su laƙume kudi bar Naira biliyan 2.67 a birnin Kano da ƙauyuka
- Daraktan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya fitar da sanarwar bayan gwamnatin Kano ta yi taron majalisar zartarwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano- Gwamnatin Kano ta ware makudan kudi domin yin wasu ayyuka na musamman a fadin jihar.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya amince da ware kudi har Naira biliyan 2.67 domin yin ayyukan.
Legit ta tattaro jerin ayyukan ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin ayyukan da gwamnatin Kano za ta yi
- Samar da ofisoshi ga ma'aikatar sufuri ta jihar Kano da masu ba Abba Kabir Yusuf shawara domin saukaka yanayin aikin gwamnati.
- Samar da cibiyar na'ura mai ƙwaƙwalwa da fasahar zamani domin bunkasa ilimi da yaki da jahilci a cikin al'ummar Kano.
- Gyara ginin Golden Jubilee Monument a babbar gadar Rabi'u Musa Kwankwaso da ke kan hanyar fadar mai martaba Sarkin Kano domin kiyaye tarihin al'adun jihar.
- Gyara magudanan ruwa da suka lalace a kan hanyar ƙananan hukumomin Shanono zuwa Gwarzo.
- Gina hanya mai nisan kilomita biyu daga kauyen Riga zuwa Karkari da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar.
- Gina dakin kwanan ɗalibai a jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke karamar hukumar Wudil a jihar Kano.
- Samar da manyan motoci guda biyar domin inganta harkar samar da ruwan sha a fadin jihar Kano.
Abba ya kaddamar da titi a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta kaddamar da ginin titin sama a kan ₦15bn a titin 'Dan Agundi domin rage cunkoson abubuwan hawa a yankin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da titin mai hawa uku domin ganin yadda za a fara gudanar da aikin da kammala shi a kan lokaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin
Asali: Legit.ng