Zanga Zanga: A Ƙarshe Ƴan Arewa Sun Jero Buƙatunsu, Sun Aika Saƙo Ga Shugaba Tinubu

Zanga Zanga: A Ƙarshe Ƴan Arewa Sun Jero Buƙatunsu, Sun Aika Saƙo Ga Shugaba Tinubu

  • Kungiyoyin Arewa sun buƙaci Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Arewa su tashi tsaye wajen warware damuwar al'umma
  • Shugaban gamayyar kungiyoyin na Zamfara, ya yi kira ga shugaban ƙasa ya sake nazari kan matakn da ya ɗauka kamar cire tallafi
  • Ya kuma roki masu zanga-zanga, shugabanni da jami'an tsaro su zama masu kishin ƙasa kuma su mutunta doka da oda

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gamayyar kungiyoyin Arewa ta yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sake nazari kan tsare-tsaren tattalin arziƙin da ta zo da su.

Kungiyoyin sun kuma buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da muƙarrabansa su kara dagewa a yaƙi da ƴan bindiga da sauran ƴan tada ƙayar baya musamman a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

Masu zanga zanga da Bola Tinubu.
Yan Arewa sun bukaci Shugaba Tinubu ya sake nazari kan matakin tattalin arzikin da ya ɗauka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Sun kuma yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa da su gaggauta ɗaukar matakin warware abubuwan da suka damu al'ummarusu, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a magance matsalolin Arewa

A cewarsu, za a iya shawo kan matsalolin Arewa ta hanyar samar da ilimi mai inganci, rage radadin talauci, tallafin sufuri da karfafa gwiwar matasa su rungumi noma maimakon zanga-zanga.

Jagoran gamayyar ƙungiyoyin Arewa (CNG) reshen jihar Zamfara, Hussaini Hassan ne ya faɗi hakan yayin ganawa da manema labarai a Gusau, rahoton Tribune Nigeria

Ya nuna damuwa kan yadda masu zanga-zanga ke daga tutar Rasha da rera wakokin nuna adawa da dimokuradiyya, suna kira ga Shugaba Putin da sojoji su karɓe Najeriya.

Hussaini Hassan ya ce dimokuradiyya a Najeriya ba ta yi abin da ya dace ba, duk da haka ya ce ana bukatar hadin kai daga dukkan 'yan Najeriya don ganin ta yi aiki. 

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da manyan hafsoshin tsaro ana tsaka da zanga zanga

Zanga-zanga: CNG ya gargaɗi ƴan Najeriya

Bisa haka ne shugaban CNG ya buƙaci ƴan Najeriya da kar su bari wasu ƴan kasashen ƙetare su yi amfani da zanga-zanga wajen ruguza ƙasar nan.

CNG ta amince cewa cire tallafin man fetur da na wutar lantarki da tsarin musayar Naira da gwamnatin Tinubu ta aiwatar ne suka jawo wahalhalun da ake ciki.

Kungiyar ta yi kira ga masu zanga-zanga, shugabannin al’umma, da jami’an tsaro su kasance masu kishin kasa da mutunta doka da oda.

Bola Tinubu ya yi naɗe-naɗe

A wani rahoton kuma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimman naɗe-naɗe a ma'aikatar jin kai da yaƙi da fatara ta tarayya.

Hakan wata alama ce da ke nuna zai yi wahala shugaban ya dawo da Dr. Betta Edu kan kujerar minista bayan dakatar da ita a watan Janairu, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262