Tsaro: Gwamnati Ta Fitar da Makudai a Watanni 6, An Kashe Naira Tiriliyan 1
- Rashin tsaro da ya zama karfen kafa a kasar nan ya na ci gaba da daukar hankali, yayin da aka gano makudan kudin da gwamnati ta kashe
- Alkaluman da aka tattaro sun nuna yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fitar da Naira Tiriliyan 1 domin yakar ta'addanci
- An gano cewa an fitar da kudin ne a cikin watannin shidan farkon shekarar 2024; daga Janairu zuwa Yuni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Yayin da rashin tsaro ya ke kamari a Najeriya, an gano yadda gwamnatin tarayya ta fitar da kudi masu nauyi domin yakar ta'addanci.
Daga watan Janairu zuwa Yuni, 2024, gwamnati ta fitar da N1.03tr domin yaki da ta'addanci a sassan Najeriya.
Jaridar Punch ta tattaro cewa kudin da aka fitar ya kai 42.80% na kasafin Naira Tiriliyan 2.41, wanda ke nufin yanzu Naira Tiriliyan 1.38 ya rage a kasafin da aka warewa bangaren tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da kasafin tsaro, Ana kashe jama'a
Alkaluman da aka tattaro sun nuna yadda ake samun karuwar hare-haren 'yan ta'adda duk da makudan kudin da gwamnati ta fitar ga bangaren.
An gano cewa zuwa yanzu, an 'yan kashe mutane 5,801 a hare-hare daban-daban, kuma an sace mutane 4,348 a watannin bakwai na farkon 2024.
Wuraren da rashin tsaro ya fi kamari
An kashe mutane da sace wadansu a kananan hukumomin kasar nan 574 daga cikin 774 da ake da su a fadin Najeriya.
Arewa maso Gabas ce ta fi fuskantar matsala inda aka kashe mutane 2,223 a hare-hare da miyagu su ka kai kananan hukumomi 88 a yankin.
Gwamnati ta tsaurara tsaro a Kano
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa tuni ta tsaurara tsaro a sassan jihar bayan sassauta dokar takaita zirga-zirga da aka sanya biyo bayan rikicin zanga-zanga.
Kwamishinan 'yan sandan Kano, Salman Dogo ne ya bayyana haka, inda ya nemi hadin kan mazauna jihar domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng