Gwamnatin Tinubu Ta Sake Magana kan Dawo da Tallafin Man Fetur da Kawo Saukin Abinci

Gwamnatin Tinubu Ta Sake Magana kan Dawo da Tallafin Man Fetur da Kawo Saukin Abinci

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana kan dawo da tallafin man fetur da yan Najeriya suka yi zanga zanga a kai saboda tsadar rayuwa
  • Ministan kudi, Wale Edun ne ya yi bayanin tare da faɗin kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa wajen shigo da tataccen man fetur
  • Haka zalika ministan ya fadi shirye shiryen da gwamnatin tarayya ke yi wajen ganin abinci ya wadata ga talakawa a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi magana kan kira da jama'a suke wajen dawo da tallafin man fetur.

Hakan na zuwa ne bayan matasan Najeriya sun shafe kwanaki shida suna zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi masu adawa da matatar man Dangote, 'yan Najeriya sun yi martani

Wale Edun
Gwamnatin Tinubu ya yi managa kan tallafin mai. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa ministan kudi na kasa, Wale Edun ne ya yi bayanin a wata hira da ya yi da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu zai dawo da tallafi mai?

Business Day ta wallafa cewa ministan kudi, Wale Edun ya ce Najeriya tana kashe $600m a kowane wata domin shigo da mai daga ƙasashen ketare.

Sai dai duk da haka, Wale Edun ya ce kasashen Afrika da suke kewaye da Najeriya ne ke cin gajiyar kudin da ake kashewa wajen karkatar da man fetur din.

Saboda haka ya ce dole sai dai yan Najeriya su yi hakuri a kan tallafin man fetur domin saboda haka ne shugaba Bola Tinubu ya cire shi.

Kokarin Tinubu wajen samar da abinci

Ministan kudi ya ce duk da cire tallafin, suna tabbatarwa yan Nijeriya za su cigaba da kula da walwalarsu musamman wajen samar da abinci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gargadi yan Najeriya bayan zanga zanga ta barke a Birtaniya

Wale Edun ya ce akwai ƙoƙarin ganin an samar da abinci daga gida da kuma bude iyakoki na wucin gadi domin shigo da kaya daga waje.

Ministan ya ce gwamnati ta yi haka ne domin ganin farashi ya sauka kuma za ta tabbatar hakan bai shafi masu noma a Najeriya ba.

Atiku ya yi maganar tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya.

Atiku Abubakar ya ce akwai lauje cikin naɗi kan yadda shugaba Bola Tinubu ya gaza yi wa ƴan kasa bayani kan lamarin tallafin man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng