Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Lokacin da Shirin Rage Farashin Abinci Zai Fara Aiki
- Gwamnatin tarayya ta yi magana kan dakatar da karɓar harajin shigo da kayayyakin abinci daga ƙasashen waje
- Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana cewa shirin zai fara aiki ne daga sati mai zuwa
- Shugaban na kwastam ya yi fatan cewa shirin zai sanya farashin kayayyakin abinci ya yi sauƙi a ƙasar nan biyo bayan tashin gwauron zabin da ya yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dakatar da harajin shigo da kayayyakin abinci daga ƙasashen waje zai fara aiki a sati mai zuwa.
A cikin watan Yuli gwamnatin tarayya ta amince da ɗage haraji na kwana 150 domin shigo da masara, shinkafa da alkama, a ƙoƙarin rage hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar nan.
Kwastam ta yi magana kan ɗage haraji
Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana lokacin da dakatar da harajin zai fara aiki ranar Talata a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi bayanin cewa tsaikon da aka samu wajen aiwatar da tsarin ya faru ne domin tabbatar da cewa an kare muradun masu ruwa da tsaki ciki har da manoma, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
Shugaban na hukumar kwastam ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara hakuri, inda ya ƙara da cewa wasu daga cikin kayayyakin waɗanda tuni aka shigo da su cikin ƙasar nan, ba za a karɓi harajinsu ba.
"Ma'aikatar kuɗi tana aiki a kan ƙa'idojin yadda za a dakatar da harajin sannan ina ba da tabbacin cewa cikin sati mai zuwa za su kammala."
"Da zarar an kammala, hukumar kwastam za ta fara aiwatar da waɗannan tsare-tsaren."
- Bashir Adeniyi
Bashir Adeniyi ya nuna fatan cewa dakatar da biyan harajin kan kayayyakin abinci da ake shigowa da su, zai taimaka wajen rage farashin kayan abinci.
Basarake ya ɗauki mataki kan tsadar abinci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya haramta ƙungiyoyi da ke cikin kasuwannin garin Ige gaba ɗayansu daga aiki.
Basaraken ya dauki matakin ne domin dakile yawan tashin farashin kaya da ya ke zargin ƙungiyoyin suna taka muhimmiyar rawa a kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng