Zanga Zanga: Matasa Sun Kai Hari Gidan Sanatan APC, Ya Yi Zazzafan Martani

Zanga Zanga: Matasa Sun Kai Hari Gidan Sanatan APC, Ya Yi Zazzafan Martani

  • Sanata Ibrahim Bomai ya yi martani bayan wasu da ake zargi suna cikin masu zanga zangar tsadar rayuwa sun kai hari gidansa
  • Sanatan mai wakiltar Yobe ta Kudu ya zargi yan siyasa a ciki da wajen jami'yyar APC da zuga matasan wajen kai hari gidansa
  • Haka zalika Sanata Ibrahim Bomai ya ambaci dalilin da yasa aka kai masa harin da kuma matakin da ya dauka bayan harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Sanatan APC mai wakiltar Yobe ta Kudu, Ibrahim Bomai ya yi magana bayan matasa sun kai hari gidansa yayin zanga zanga.

Sanata Ibrahim Bomai ya yi zargin cewa an zuga matasan ne kan su kai hari gidansa duk da cewa ba su da niyyar yin hakan a karon farko.

Kara karanta wannan

'Za mu dawo': APC ta tsure, matasan da suka kona sakatariya sun tura sakon barazana

Sanata Bomai
Masu zanga zanga sun kai hari gidan Sanata a Yobe. Hoto: Ibrahim Mohammed Bomai
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'in Sanatan mai suna Abubakar Madu Bukar ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bomai: 'An zuga matasa su farmaki gidana'

Jaridar 21st Cetury Cronicle ta wallafa cewa Sanata Ibrahim Bomai ya zargi yan adawa da makiya da zuga matasa wajen kai hari gidansa da ke jihar Yobe.

Ibrahim Bomai ya ce hakan ya faru ne kasancewar gidansa ba ya kan hanyar da matasan suke bi wajen yin zanga zangar.

Ya kuma bayyana cewa akwai gidajen yan siyasa guda hudu a kan layin gidan nasa amma ba a taba kowane gida ba sai na shi.

Sanata Bomai zai cigaba da ƙoƙari

Jami'in Sanata Ibrahim Bomai, Abubakar Madu Bukar ya ce harin ba zai sa Sanatan ya rage ƙoƙari da yake a jihar ba.

Haka zalika Abubakar Madu Bukar ya ce Sanatan ya ce masu son ganin bayansa a jam'iyyar APC da sauran jam'iyyu ba za su yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa na daukar nauyin zanga zanga? an gano gaskiya

Har ila yau, Sanatan ya ce maganar kawo cigaba a yankin Yobe ta Kudu kuma yanzu ya fara, babu gudu babu ja da baya.

An bukaci Sanata Akpabio ya yi murabus

A wani rahoton, kun ji cewa kalaman da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya yi kan zanga-zanga na ci gaba da tayar da ƙura a ƙasar nan.

Wani babban jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Neja ya buƙaci Akpabio da ya yi murabus daga muƙaminsa sannan ya ba ƴan Najeriya haƙuri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng