Matsala ta Taso: Dangote na Shirin Saida Wani Kason Hannun Jarin Matatar Mansa
- Sakamakon wata matsalar kudi ko dalilinsu a kasuwar hada-hada, akwai yiwuwar Dangote ya sayar da kaso 12.75 na hannun jarin matatar mansa
- Wata hukumar tantance lamuni ta ce Dangote na bukatar kudin domin biyan wani babban bashi da wa'adinsa ke karewa karshen Agusta
- Hannun jarin da Dangote zai sayar na daga cikin kaso 12.75 da kamfanin NNPC ya bari a lokacin da ya ce ya sayi hannun jarin kaso 20 a 2021
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
'Fitch Ratings', wata hukumar tantance lamuni, ta ce Aliko Dangote na shirin sayar da kashi 12.75 na hannun jarin matatar man Dangote saboda matsalar kudi ko dalilinsu.
An ce Dangote na shirin yin amfani da kudin da ya samu daga hannun jarin da zai sayar domin biyan wani lamuni mai yawa wanda wa'adinsa zai cika a ranar 31 ga Agusta, 2024.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar Fitch ta fitar a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harkallar NNPCL da Dangote a 2021
A watan Satumbar 2021, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya sayi kashi 20 na hannun jarin matatar Dangote kan dala biliyan 2.76.
Sai dai kuma, a ranar 14 ga watan Yuli, Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka, ya ce iya kashi 7.2 na hannun jarin matatarsa ne NNPC ya mallaka a yanzu.
A cewar hukumar Fitch, harkallar da aka yi a 2021 ta nuna cewa NNPC na da mallakin kaso 7.25 na matatar man Dangote a kan kudi dala biliyan 1, amma da zabin sayen kaso 12.75 zuwa Yunin 2024.
Dangote na shirin biyan bashi a Agusta
Tun da har kawo yanzu NNPC bai sayi sauran ragowar kaso 12.75 na hannun jarin ba, Fitch ya ce rukunin kamfanonin Dangote na da shirin sayar da kason a wannan shekarar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito hukumar tantancen lamunin na cewa:
"Rukunin kamfanonin zai biya wani bashi mai yawa a karshen watan Agustan 2024 daga kudin da aka samu. Sai dai kuma babu tabbaci kan ko Dangote zai iya biyan bashin a kan lokaci."
Matsalar kudin da Dangote ke fuskanta
Hukumar Fitch ta ce tun daga shekarar 2023 kamfanin Dangote (DIL) ya hada bayanan kudi ko dalilinsu wanda ya kunshi Naira tiriliyan 1.4 na tsabar kudi (wanda ba a tantance su ba).
"Bugu da ƙari, akwai yiwuwar ƙarin tabarbarewar lamura a FCF saboda sauye-sauye a kasuwar hada-hadan kudin ketare da kuma buƙatun jari a cikin 2024 da 2025.
"Kudi ko dalilinsu da kamfanin ke da shi a kasa ba zai iya magance matsalar bashin gaba ba. Kamfanin na son sayar da kaso 12.75 na hannun jarin matatar man domin biyan bashin."
- A cewar Fitch.
Obasanjo ya magantu kan matatar Dangote
A wani labarin, mun ruwaito cewa Olusegun Obasanjo ya ce masu samun kudi ta hanyar fita da shigo da mai ba za su bari matatar man Dangote ta yi nasara ba.
Tsohon shugaban Najeriya ya kamata ya yi ace 'yan Najeriya su yi murna da zuwa matatar Dangote kasancewa za ta jawo masu zuba jari daga ciki da wajen kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng