NNPC: Gwamnati za ta saye hannun jari a kamfanin Dangote, hakan bai masa dadi ba

NNPC: Gwamnati za ta saye hannun jari a kamfanin Dangote, hakan bai masa dadi ba

  • Shugaban kamfanin NNPC ya ce za su saye hannun jari a matatar Aliko Dangote
  • Yanzu haka ana kokarin gina wannan katafaren kamfani da ke Lekki, jihar Legas
  • Mele Kolo Kyari ya ce Gwamnatin Tarayya na shirin mallakar 20% a kamfanin

Babban darektan kamfanin mai na kasa watau NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce Aliko Dangote bai so ya saida hannun jarin matatar da yake gina wa a garin Legas.

Mele Kolo Kyari ya ce ya na da kyau kamfanin NNPC ya zuba hannun jari a kamfanin na Dangote, saboda gwamnati ta samu ta-cewa a matatar da ake gina wa.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto, shugaban NNPC din ya ce NNPC za ta saye 20% na hannun jarin da kamfanin attajirin ‘dan kasuwan ya mallaka.

KU KARANTA: Lauretta Onochie ‘Yar APC ce ta-a-mutu, ba ta mukami hadari ne - PDP

Jawabin shugaban kamfanin NNPC

Nairmaterics ta rahoto Kyari ya na cewa:

“Babu kasar da za ta zura idanu a rika irin wannan kasuwanci, wanda ya shafi harkar mai, wanda yake da hadari. Sai ka tsaya kurum ka na kallo”
“An ba mu dama, amma ban tabbatar ko Aliko Dangote zai so ya saida hannun jarinsa a kamfanin ba. Zan iya cewa mu ne mu ka kawo maganar saida hannun jarin, bai so ya saida na shi hannun a matatar."

Mele Kyari ya ce NNPC za ta sa hannu a harkar kasuwancin taki, mai, gas da kananan matatun danyen mai, domin fadada inda gwamnatin tarayya ta shiga.

“Ba na tunanin Dangote zai yi murna sosai da wannan. Za mu dauki 20% na kamfanin tace mansa, akwai hanyar da za a bi ayi wa kamfaninsa daraja a kasuwa.”

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun gagara ceto Sarkin Eda-Ile, an biya N2m

Mele Kolo Kyari
Shugaban kamfanin NNPC
Asali: UGC

Malam Kyari yake cewa babu bankin da zai ba NNPC aron wadannan kudi har Naira biliyan 19 kai-tsaye, sai sun nemi taimakon majalisar zartarwa ta tarayya, FEC.

“Mu na alfahari da tsarin, zai taimaka wa masu ruwa da tsakin-mu, har da daukacin mutanen Najeriya mutum miliyan 200 da za su yi murnar sayen hannun jarin.”

Dazu kun ji gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce duk Gwamnan da ya bar PDP bayan ta yi masa riga-da-wando, ya ci amana, ganin Bello Matawalle ya koma APC.

Nyesom Wike ya ce gwamnonin da suke sauya-sheka zuwa APC ba su san abin da ya kamata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel