Hukumar Kwastam Ta Bayyana Abin da Zai Jawo a Samu Saukin Farashin Abinci

Hukumar Kwastam Ta Bayyana Abin da Zai Jawo a Samu Saukin Farashin Abinci

  • Hukumar kwastam ta ƙasa ta tabbatar da cewa an janye harajin shigo da wasu kayayyaki daga ƙasashen ketare zuwa Najeriya
  • Shugaban hukumar na kasa, Bashir Adeniyi ne ya bayyana haka, inda ya ce ana sa ran matakin zai ruguzo da farashin kayayyaki
  • shugaban na wannan batu a daidai ranar da 'yan Najeriya su ke cikin rana ta shida da zanga-zangar kin jinin hauhawar farashi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban hukumar kwastam na ƙasa, Bashir Adeniyi ya ce ana sa ran za a samu saukar farashin kayayyaki nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da manyan hafsoshin tsaro ana tsaka da zanga zanga

Shugaban na ganin za a samu saukar farashin da ya daɗe ya na hauhawa ne saboda dakatar da haraji a kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su daga ketare.

Bashir
Hukumar kwastam ta ce janye harajin shigo da kaya zai sauko da farashi Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwastam ta bayyana haka ne ga taron shugabannin hukumomin tsaron Najeriya a wani zama da aka gudanar ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu tabbatar da kudurin gwamnati," Kwastam

Hukumar kwastam ta bayyana cewa za ta tabbatar an aiwatar da sababbin kudurorin gwamnati a hukumar. Bashir Adeniyi da ya bayyana haka ya ce daga cikin tsare-tsaren akwai janye harajin shigo da kaya, Channels Television ta wallafa.

Kwastam: "Dalilin janye harajin shigo da kaya"

Hukumar kwastam ta ƙasa ta ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta saurari koken yadda farashin abinci ya yi tashin gwauron zabo, shi ya sa ta dakatar da haraji.

Kara karanta wannan

"Babu ruwanmu," Gwamnati ta kare kanta bayan tangardar intanet da rufe layukan waya

Shugaban hukumar, Bashir Adeniyi ya ce da yawa daga cikin abincin kasar nan shigowa ake yi da su daga ketare, saboda haka matakin zai yi kyau.

Kwastam ta kama lalatattun magunguna

A wani labarin kun ji yadda hukumar kwastam ta lalatattun magunguna da abinci marasa kyau da ake kokarin shigowa da shi cikin kasar nan.

Shugaban hukumar na Apapa, Babatunde Olomu da ya bayar da tabbacin ya ce an kama katon 7,580 na rubabben naman kaji na kimanin N424m.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.