Ana Cikin Zanga Zanga, Gwamna Ya Fadi Mafi Karancin Albashin da Zai Biya Ma'aikata

Ana Cikin Zanga Zanga, Gwamna Ya Fadi Mafi Karancin Albashin da Zai Biya Ma'aikata

  • Gwamnatin jihar Ondo ta shirya domin fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashin N70,000 duk wata
  • Shugaban ma'aikatan jihar ya bayyana cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya amince zai biya sabon mafi ƙarancin albashin ga ma'aikatan jihar
  • Matsayar gwamnatin na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar sabon mafi ƙarancin albashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta amince da biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi.

Gwamnatin Ondo za ta biya albashin N70,000
Gwamna Lucky Aiyedatiwa zai biya mafi karancin albashin N70,000 Hoto: Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Shugaban ma'aikatan jihar, Bayo Philip, ya bayyana hakan a birnin Akure, babban birnin jihar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abu 1 da ba zai lamunta ba a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa Gwamna Aiyedatiwa zai biya ma'aikatan Ondo?

Bayo Phillip ya ce Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta biya wani abu ba ƙasa da abin da gwamnatin tarayya ta amince da shi a matsayin mafi ƙarancin albashin.

Shugaban ma'aikatan ya ce gwamnatin jihar a shirye take ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin wanda Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Yayin da yake nanata ƙudirin gwamnan na kyautata jin dadin ma’aikatan jihar, ya bayyana cewa jihar Ondo ita ce ta fara biyan tallafin N35,000 ga ma’aikata.

"Kafin shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu kan ƙudirin, gwamna ya ba da tabbacin cewa jihar Ondo za ta biya ko wane irin mafi ƙarancin albashi aka amince da shi kuma shugaban ƙasa ya sanya masa hannu."

Kara karanta wannan

Babban lauya ya ba Tinubu lakanin kawo karshen zanga zangar da ake yi

-.Bayo Philip

Gwamna Sule zai biya albashin N70,000

A wani labarin kuma, kun ji Gwamna Abdullahi Sule ya ce ya gama shirin fara biyan N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a Nasarawa.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Peter Ahemba ya bayyana cewa tuni Sule ya amince da biyan sabon mafi karancin albashin wanda za a fara nan ba da dadewa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng