Ba a Gama da Dangote ba, Obasanjo Ya Tono Batun Cin Hanci a Matatun Najeriya
- Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan matatun man Najeriya da yadda ya yi fama da su a lokacin mulkinsa
- Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya mikawa kamfanin mai na Shell ragamar matatun man Najeriya amma suka ƙi yarda lokacin
- Haka zalika Obasanjo ya yi magana kan yadda yan siyasa ke yin alkawarin gyara matatun ba tare da cika alkawarin ba a tsawon shekaru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda cin hanci ya dabaibaye harkar mai a Najeriya.
Cif Olusegun Obasanjo ya fadi haka ne yayin da yake magana a kan yadda matatun man fetur suka gaza gyaruwa a Najeriya tsawon shekaru.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Obasanjo ya nufi mika matatun man Najeriya ga yan kasuwa domin lura da su amma suka ƙi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cin hanci a harkar matatun mai
Cif Olusegun Obasanjo ya labarta cewa ya yi yunkurin mika matatun man fetur din Najeriya ga kamfanin Shell domin lura da su.
Amma kamfanin ya ki amincewa a wancan lokacin tare da cewa cin hanci da rashawa sun dabaibaye harkar matatun mai a Najeriya.
Bayan haka, jami'an kamfanin sun bayyana cewa ba za su so shiga harkar matatun ba saboda ba a dauko kwararru domin lura da su ba.
Gyaran matatun man Najeriya ya gagara
The Cable ta wallafa cewa Olusegun Obasanjo ya ce yan siyasa sun dauki shekaru suna alkawarin gyaran matatun man fetur amma har yanzu shiru ake ji.
Tsohon shugaban kasar ya ce har yanzu matsalolin da suka dabaibaye harkar matatun mai ne suka hana ruwa gudu kuma suna nan suna karuwa.
A karshe, Obasanjo ya ce matuƙar ba a tsaya an magance irin matsalolin ba, ba lallai a samu wani cigaba a Najeriya ba.
Matatar Dangote: Obasanjo ya yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa masu cin gajiyar shigo da mai za su yi kokarin cin dunduniyar matatar Dangote.
Olusegun Obasanjo ya idan har ta samu nasara, to ya kamata matatar Dangote ta zamo abin alfahari da zama tsani ga masu zuba jari a gida da waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng