Zanga Zanga: Kungiyar ECOWAS Ta Tsoma Baki Kan Halin da Najeriya Ke Ciki

Zanga Zanga: Kungiyar ECOWAS Ta Tsoma Baki Kan Halin da Najeriya Ke Ciki

  • Yayin da ake cigaba da zanga-zangar halin kunci a Najeriya, Kungiyar ECOWAS ta yi magana kan lamarin
  • Kungiyar ta jajantawa iyalai da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu da dukiyoyi yayin zanga-zangar
  • ECOWAS ta yabawa jawabin da Bola Tinubu ya yi inda ta bukaci masu zanga-zangar su ji shawarar da ya ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kungiyar ECOWAS ta tsoma baki kan zanga-zanga da ake cigaba da yi a Najeriya na tsawon kwanaki shida.

Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda aka yi ta samun tashe-tashen hankula da rasa rayuka da dukiyoyi.

ECOWAS ta yi magana kan zanga-zanga a Najeriya
Kungiyar ECOWAS ta nuna damuwa kan tashin hankula yayin zanga-zanga a Najeriya. Hoto: Ecowas - Cedeao.
Asali: Facebook

ECOWAS ta yi magana kan zanga-zanga

Wannan na kunshe ne a cikin wata da kungiyar ta fitar a shafinta na X a yau Talata 6 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnatin Kano ta ɗauki matakai 6, ta yi magana kan ɗaga tutar Rasha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ECOWAS ta nuna alhini tare da jajantawa wadanda suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da ake yi.

Zanga-zanga: ECOWAS ta ba da shawara

"Kungiyar ECOWAS na bibiyar abubuwan da ke faruwa da kuma nuna damuwa kan rikici da rasa rayuka da kuma satar kayan jama'a da ake yi, ECOWAS tana jajantawa iyalan wadanda suka mutu da al'umma da Najeriya baki daya."
"ECOWAS tana sane da 'yancin 'yan kasa na yin zanga-zanga kamar yadda yake a dokokinta da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999."
"ECOWAS ta yaba da jawabin Bola Tinubu, muna bukatar masu zanga-zanga su ji shawarar shugaban wurin tattaunawa da kuma samar da zaman lafiya."

- ECOWAS

ECOWAS ta yi martanin ne yayin da aka shiga rana ta shida ana zanga-zanga a Najeriya kan halin kunci.

ECOWAS da zanga-zangar EndSARS

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Manyan 'yan siyasa da kungiya da suka kushe jawabin Tinubu

A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa Kotun kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta take hakkin dan Adam a zanga-zangar

Kotun ta ce gwamnatin ta ci zarafin Obianuju Catherine Udeh da wasu mutane biyu yayin zanga-zangar a shekarar 2020.

Kotun ta samu Gwamnatin Najeriya da saba dokar kare hakkin dan Adam ta African Charter sashe na 1, 4, 6, 9 da kuma 10.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.